Dakarun Sojin Najeriya Sun Gano Masana'antar Kera Makamai a Jihar Kaduna
- Dakarun sojin Najeriya sun gano wata masana'antar ƙera bindigu a ƙaramar hukumar Jema'a da ke kudancin Kaduna
- Sojojin sun kama wani hatsabibin mai sayar da makamai da suka jima suna nema ruwa a jallo, sun kama wani a masana'antar
- Kwamandan rundunar Operation Save Haven ya jinjina wa dakarun sojin kana ya ce zasu kamo sauran waɗanda suka arce
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kaduna - Rundunar sojin Operation Save Haven ta bankaɗo wata masana'antar ƙera bindigogi a garin Kafanchan, ƙaramar hukumar Jema'a a jihar Kaduna.
Rundunar sojin ta samu wannan nasara ne sakamakon bin diddigi da leƙen asiri na tsawon mako ɗaya, wanda ya yi sanadin kama wani hatsabibi, Napoleon John.
John na ɗaya daga cikin mutanen da rundunar OPSH ke nema ruwa a jallo bisa zargin hannu a tada zaune tsaye da kuma sayar da makamai a jihar Kaduna.
Bayan ya shiga hannu, ya tabbatar da irin ɗanyen aikin da yake da hannu a ciki kana ya jagoranci dakarun soji zuwa wata masana'antar ƙera makamai.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wannan nasara da sojojin suka samu na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar sojin Najeriya ta wallafa a shafinta na Manhajar X ranar Jumu'a, 22 ga watan Satumba.
Sojojin sun kama wani Monday Duniya a masana'antar wanda ya tabbatar da cewa ya shafe sama da shekaru biyar yana sana'ar ƙera bindiga da siyarwa a Kaduna da Filato.
Sanarwan hukumar sojin ta ce:
"Binciken da muka yi a masana’antar ya nuna wasu tarin makamai, da suka hada da, bindigogi kirar AK-47 na gida, da bindigu kirar AK-47 na soja, bindigu masu sarrafa kansu, da dai sauransu."
Kwamanda ya yaba wa dakarun soji
Yanzu-Yanzu: An Kammala Binciken Gawar Fitaccen Mawakin Nan Da Ka Tono Daga Ƙabari, Bayanai Sun Fito
Da yake jinjinawa sojojin, kwamandan rundunar OPSH, ya sha alwashin cewa dakaru ba zasu yi ƙasa a guiwa ba wajen kamo sauran abokan aikin 'yan ta'addan da suka arce.
Janar AE Abubakar ya kuma gode wa ɗaukacin al'umma bisa goyon bayan da su ke bai wa sojoji a yaƙin da suke yi kana ya roƙi su ci gaba da taimaka wa da bayanan sirri.
'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Fasto, Ɗiyarsa da Wani Mutum Daya a Kalaba
A wani rahoton na daban 'Yan bindiga sun yi awon gaba da Malamin addinin Kirista da ɗiyarsa da wani mutum ɗaya a Kalaba, jihar Kuros Riba.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun sace abin harinsu a jirgin ruwa da misalin ƙarfe 8 zuwa 9 na daren ranar Alhamis.
Asali: Legit.ng