Gwamnatin Kebbi Ya Haramta Ayyukan Hako Ma'adanai, Ta Rufe Wuraren Aikin a Jihar

Gwamnatin Kebbi Ya Haramta Ayyukan Hako Ma'adanai, Ta Rufe Wuraren Aikin a Jihar

  • Gwamnatin Nasiru Idris ta jihar Kebbi ta haramta ayyukan haƙo ma'adanai a faɗin jihar da ke Arewa maso Yammacin Najeriya
  • Sakataren gwamnatin Kebbi, Yakubu Tafida, ya ce an ɗauki wannan matakin ne saboda yanayin taɓarbarewar tsaro a jihar
  • Ya ce gwamnati ta fi ɗaukar tsaron al'umma da su kansu ma'aikatan wuraren haƙo ma'aidanai da muhimmanci

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kebbi - Gwamnatin jihar Kebbi ƙarƙashin jagorancin gwamna Nasiru Idris ta haramta dukkan ayyukan haƙo ma'adanai a faɗin jihar, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Sakataren gwamnatin jihar da ke Arewa maso Yamma, Yakubu Tafida, ne ya bayyana haka yayin da yake jawabi ga 'yan jarida a Birnin Kebbi, ranar Jumu'a.

Gwamnan jihar Kebbi, Nasiru Idris.
Gwamnatin Kebbi Ya Haramta Ayyukan Hako Ma'adanai, Ta Rufe Wuraren Aikin a Jihar Hoto: Kebbi State Today
Asali: Facebook

Ya ce gwamnati ta dauki wannan mataki ne saboda taɓarɓarewar tsaro da kuma bukatar kare rayukan ma’aikatan da ke hakar ma’adanai, da garuruwan da ke karɓan bakuncinsu.

Kara karanta wannan

Nasara Daga Allah: Jami'an Tsaro da Mutanen Gari Sun Halaka 'Yan Bindiga Sama da 20 a Jihar Arewa

Meyasa gwamnati ta ɗauki wannan matakin?

Ya bayyana hakan a matsayin matakin riga-kafi da nufin tabbatar da tsaron ma’aikata da mutanen da ke rayuwa a cikin garuruwan da ake hakar ma’adinai.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tafida ya ƙara da cewa gwamnatin tana sane haƙar ma’adinai na karkashin keɓantaccen jerin dokoki ba, amma ta dauki matakin ne bayan ta yi nazari sosai kan yanayin tsaro da ake ciki.

SSG ya ce gwamnati ta yi imanin cewa yana da matukar muhimmanci ta ba da fifikon kariya da tsaron lafiyar jama'a tare da daƙile yunkurin wasu bara gurbi na maida wurin wajen aikata laifuka.

"Wannan ya faru ne a wasu jihohin da ke makwabtaka da mu wanda a yanzu muke son kaucewa," in ji shi

A cewarsa, gwamnati ta yanke shawarar magance matsalolin ta hanyar tantancewa da kuma gindaya tsauraran matakai da ka'idoji da nufin inganta aikin haƙo ma'adinai.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Kotun Zabe Ta Kwace Kujerun 'Yan Majalisa 3 Na PDP, Ta Faɗi Waɗanda Suka Ci Zaɓe

Sakataren ya kuma yi bayanin cewa ta haka ne za a kiyaye muhalli, inganta samar da kudaden shiga da kuma uwa uba samar da tsaro ga al'umma, rahoton Daily Trust.

Kotun Zabe Ta Ƙara Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamnan Arewa

A ɗazu kun ji cewa Kotun zaɓe mai zama a Jos ta tabbatar da nasarar gwamna Celeb Mutfwang na jam'iyyar PDP a zaben jihar Filato.

Da take yanke hukunci ranar Jumu'a, Kotun ta ce ɗan takarar APC ba shi da hurumin kalubalantar harkokin da suka shafi PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262