Yan Sanda Sun Kammala Bincike Kan Gawar Mawaki Mohbad a Jihar Legas
- Rundunar 'yan sanda ta bayyana cewa an gama binciken gawar fitaccen mawakin nan Mohbad a jihar Legas
- Kakakin 'yan sanda na jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya ce a halin yanzun ana dakon sakamakon binciken gawar daga likitoci
- A ɗazu ne hukumar 'yan sanda da tawagar jami'an lafiya suka tono gawar mawaƙin daga ƙabarinsa
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Legas - Rundunar ‘yan sanda ta sanar da cewa ta kammala binciken gawar marigayi fitaccen mawaki nan, Ilerioluwa Aloba wanda aka fi sani da Mohbad.
Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sanda reshen jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, shi ne ya tabbatar da haka a shafinsa na manhajar X, wanda a baya ake kira Twitter.
A wani ɗan gajeren saƙo da kakakin 'yan sandan ya wallafa da daren ranar Alhamis, 21 ga watan Satumba, 2023, ya ce an kammala binciken gawar suna jiran sakamako.
Hundeyin ya rubuta cewa, "An kammala binciken gawa, muna jiran sakamako."
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Idan baku manta ba mun kawo muku rahoton yadda rundunar ‘yan sandan jihar Legas tare da wasu jami’an lafiya suka tona ƙabarin Mawakin, suka ciro gawarsa a yau Alhamis.
Abubuwan da suka biyo bayan rasuwar Mohbad
Allah ya yi wa Mawakin rasuwa ne ranar 12 ga watan Satumba, 2023 kuma an ɓinne gawarsa washe gari a Anguwar Ikorodo da ke jihar Legas a Kudu maso Yammacin Najeriya.
Wannan mutuwa ta farat ɗaya da Mohbad ya yi a tada hazo a sassan Najeriya, inda mutane da dama da masoyansa suka fito kan tituna zanga-zangar neman a kamo waɗanda suka kashe shi.
Jim kaɗan bayan mutuwarsa, shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, IGP Kayode Egbetokun, ya umarci a gudanar da bincike kan maƙasudin abinda ya yi ajalinsa.
Majalisar dattawa ta tura wakilai zuwa gidan Mohbad domin yi wa matarsa, iyalansa da sauran yan uwa da masoya ta'aziyyar wannan babban rashi.
DSS Ta Kama Dan Majalisar PDP Bisa Zargin Hannu a Kashe-Kashe
A wani rahoton kuma Hukumar DSS ta kama mamban majalisar dokokin jihar Ogun da wasu mutum 5 bisa zargin hannu a kashe rayuka sama da 20 a Sagamu
Jami'an tsaron farin kaya suna zargin ɗan majalisar na jam'iyyar PDP da hannu a rura wutar rikicin ƙungiyoyin asiri
Asali: Legit.ng