Yan Sanda da Jami'an Lafiya Sun Tono Gawar Mawaki Mohbad Daga Kabari

Yan Sanda da Jami'an Lafiya Sun Tono Gawar Mawaki Mohbad Daga Kabari

  • 'Yan sanda da jami'an lafiya tona ƙabarin fitaccen Mawakin nan Mohbad, sun ciro gawarsa domin gudanar da bincike
  • Ilerioluwa Aloba wanda aka fi sani da Mohbad ya mutu ne ranar 12 ga watan Satumba, 2023 kuma aka ɓinne shi washe gari
  • Mutuwar mawakin ya tada hazo mumman daga masoyansa waɗanda suka nemi rundunar 'yan sanda ta kama makasan da suka kashe shi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Lagos - Rundunar 'yan sanda reshen jihar Legas tare da wasu jami'an lafiya sun tono gawar fitaccen mawaƙin nan, Ilerioluwa Aloba, wanda aka fi sani da Mohbad.

Jami'an hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan reshen jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da tono gawar domin gudanar da bincike a shafinsa na Manhajar X.

Yan sanda sun tono gawar Mohbad a jihar Legas.
Yan Sanda da Jami'an Lafiya Sun Tono Gawar Mawaki Mohbad Daga Kabari Hoto: Policeng
Asali: UGC

Kakakin 'yan sandan ya wallafa a shafinsa cewa:

Kara karanta wannan

Hawaye Sun Kwaranya Bayan Miyagu Sun Halaka Fitaccen Dan Jarida a Najeriya

"An kammala aikin tono gawar marigayi Mohbad, yanzu kuma za a fara gudanar da bincike."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shahararren Mawakin ya rasu ne a ranar 12 ga Satumba, 2023, kuma an binne shi a unguwar Ikorodu da ke Legas, washe gari.

Mutuwar mawaƙin dai ta janyo cece-kuce daga magoya bayansa waɗanda tun daga lokacin suka fantsama kan tituna suna zanga-zanga a jihohin Legas da Ogun da wasu sassan ƙasar nan.

Masu zanga-zangar sun buƙaci rundunar 'yan sandan Najeriya ta binciko tare da cafke waɗanda suka kashe Mohbad.

IGP ya umarci yan sanda su gano abinda ya yi ajalin Mohbad

Bayan rasuwarsa, Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya (IGP) Kayode Egbetokun, ya bada umarnin gudanar da bincike don gano musabbabin mutuwar mawaƙin.

Bisa umarnin IGP, kwamishinan ‘yan sandan jihar Legas, Idowu Owohunwa, ya kafa tawagar mutane 10, ciki har da likitan cututtuka, domin su tono tare da gudanar da bincike kan gawar Mohbad.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Halaka Sojoji da 'Yan Sanda Da Dama a Jihar APC

Owohunwa, wanda ya jagoranci tawagar zuwa wurin da aka binne gawar, ana kuma sa ran zai ziyarci mahaifin Mohbad a gidansa na Ikorodu.

Kotun Zabe Ta Ƙara Yanke Hukunci Kan Ƙarar da Aka Kai Gwamnan PDP

Rahoto ya nuna Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaben gwamnan ta sanar da hukuncinta kan zargin da ake wa gwamnan Enugu na amfani da takardar NYSC ta jabu.

Ɗan takarar gwamnan jihar a inuwar jam'iyyar Peoples Redemption Party (PRP), Christopher Agu, shi ne ya shigar da ƙarar gaban Kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262