“Ya Yi Kama Da Takoni”: Takalman Wani Mutum Sun Sa Ya Yi Fice Yayin da Bidiyonsa Ya Yadu a Intanet
- Wani mutum ya halarci taron jama'a sanye da kwat da wando, amma abun da ya fi jan hankalin mutane a kansa sune takalmansa
- A cikin wani bidiyon TikTok, an gano mutumin a wani wuri mai kama da mashaya yana hira a cikin abokansa
- Da suke martani ga bidiyon, mutane sun ce basu taba ganin irin wannan takalman ba tun da aka haife su
Wani mutum ya yi fice sosai a dandalin TikTok bayan wani bidiyo ya hasko dogayen takalman da ya sanya a kafafunsa.
A cikin bidiyon wanda @omotonso_1 ya wallafa, an gano mutumin cikin mutane a wani wuri da ya yi kama da mashaya.
Ya mayar da hankali wajen shaye-shaye da hira da abokansa cikin raha lokacin da aka dauki bidiyon.
Bidiyon ya fi mayar da hankali a kan dogayen takalmansa, wadanda suka yi kama da an kera masa su ne na musamman saboda kafafuwansa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Yayin da kamarar ta hasko shi, mutumin bai nuna damuwa ba ganin cewa takalmansa sun ja hankalin mutane.
Wasu da suka kalli bidiyon a TikTok sun ce basu taba ganin irinsa ba. Wasu kuma sun ce takalman sun yi kama da takobi.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani kan dogayen takalman wani mutum
@beatricelouis08 ta ce:
"Idan da ace malamin lissafina ya yi amfani da wannan takalman wajen bayanin 'longtitude' a wancan lokacin, da na ci jarrabawa."
@TICH ya yi martani:
"Wannan ba takalmi bane. Takobi kenan guda kenan."
@justlife ya ce:
"Amma a ina mutane ke samo irin wadannan takalman."
@QUEEN ta ce:
"Takalman kada."
@tolulope.oloko ta yi martani:
"Ga dukkan alamu wannan takalmin ne hanyar sufurinsa."
Abun Al'ajabi: Wani Bawan Allah Da Ya Roki Allah Dala Miliyan Ya Samu Kuɗi a Bidiyo
A wani labari na daban, wani mutumi ɗan Najeriya, wanda ya halarci taron wa'azi za aka saba yi a watan Azumin Ramadan da yamma, ya ɗaga hannu ya roki Allah SWT ya ba shi dala miliyan $100m.
Mutumin, wanda ya roƙi Allah bil hakki da gaskiya ya ba shi waɗan nan makudan kudaɗe, bai san wannan addu'a zata buɗe masa ƙofar samun taimako daga hannun bayin Allah ba.
Asali: Legit.ng