Yan Fansho a Lagas Za Su Fara Azumi a Ranar Alhamis

Yan Fansho a Lagas Za Su Fara Azumi a Ranar Alhamis

  • Yan fansho a jihar Lagas sun mika lamuransu ga Allah ta hanyar yin azumi da addu'o'i
  • A kokarinsu na ganin an gyara tsarin fansho, masu karbar fanshon za su fara azumi a ranar Alhamis, 21 ga watan Satumba
  • Sun yi zargin cewa wadanda ke a tsohon tsarin fansho sun fi kwasar garabasa sama da su da ke a sabon tsarin fansho

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Lagas - Domin cimma bukatunsu na ganin an gyara duk wasu kura-kurai a tsarin fansho na 'CPS', masu karbar fansho a jihar Lagas za su fara azumi da addu'o'i a ranar Alhamis.

Kamar yadda jaridar Punch ta rahoto, Shugaban kungiyar yan fansho na kasa reshen jihar Lagas, Michael Omisande, ne ya bayyana hakan a cikin sakon da ya saki.

Yan fansho a Lagas za su fara azumi
Yan Fansho a Lagas Za Su Fara Azumi a Ranar Alhamis Hoto: @jidesanwoolu
Asali: Twitter

Yan fansho za su yi taron addu'o'i a fadin jihar Lagas

Kara karanta wannan

Yadda Likita Ya Yanke Jiki Ya Mutu Bayan Ya Shafe Tsawon Awanni 72 Yana Aiki a Asibitin LUTH

Shugaban kungiyar ya bayyana cewa yan fansho za su yi taron addu'o'in da misalin karfe 11:00 na safe a gaba daya ofishoshin hukumar fansho da ke jihar, rahoton Business Day.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yan fansho a karkashin tsarin 'CPS' suna a sabon tsarin fansho da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya kafa a 2004 don domin gyara kurakuran da ke cikin tsohon tsarin fansho.

A karkashin sabon tsarin fansho, ana sa ran masu daukar aiki da ma'aikata su hada kudi a asusun ritaya, sannan idan suka yi ritaya ana biyan su kudin sallama yayin da za a dunga biyansu sauran duk wata.

A halin yanzu, tsohon tsarin fansho shine ya fi fa'ida, inda yan fansho ke karbar kudin sallama da fansho na muddin rayuwa.

Wadanda ke a sabon tsarin fansho a jihar Lagas sun bayyana cewa takwarorinsu da ke karkashin tsohon tsarin sun fi su jin dadi.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Dattawan Kasar Yarabawa Sun Tubewa Obasanjo Rawanin Sarautar Balogun Na Owu Da Wasu Sarautun

Omisande ya ce:

"Darakta a karkashin tsohon tsarin yana karbar sama da N250,000 yayin da takwaransa da ke cikin sabon tsarin ke karbar akalla N70,000. Gwamnatin ta gabatar da tsarin a jihar Lagas da alkawarin cewa zai fi inganci.
"Ma'aikatan Lagas sun rungume shi sannan da zuwan tsarin, wannan gwamnatin ta cire dukkanin abubuwan da za su sa tsarin ya inganta kamar su kudin sallama, rashin aika ribar da aka tara tun shekarar 2007 zuwa cikin asusun da kuma jinkirin biyan kudi kusan shekaru uku zuwa biyar. Duk wadannan abubuwan da ba su dace ba sun sa tsarin ya gaza da zuwansa."

Ya kuma bayyana cewa wasu da suka yi ritaya wadanda suka shiga sabon shirin sun koma ga tsohon tsarin saboda sharudan da aka shimfida.

Tsohon gwamnan jihar Neja ya nemi a dakatar da fansho dinsa

A wani labarin kuma, tsohon gwamnan jihar Neja kuma sanata mai wakiltan Neja ta arewa a yanzu, Abubakar Sani Bello, ya bukaci a dakatar da fansho da sauran alawun da tsoffin gwamnonin jihar ke cin moriya.

Kamar yadda jaridar Leadership ta rahoto, Sanata Bello ya bukaci hakan ne a cikin wata wasika da ya aikewa gwamnatin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng