Abinda Ministan Kwadago Ya Fada Mana Kan Sabon Mafi Karancin Albashi, TUC

Abinda Ministan Kwadago Ya Fada Mana Kan Sabon Mafi Karancin Albashi, TUC

  • Ƙungiyar TUC ta bayyana abinda Ministan Kwadago ya faɗa mata game da ƙarin albashi ga ma'aikata
  • Shugaban TUC na ƙasa, Festus Osifo, ya ce Lalong ya ce musu ya zauna da shugaba Tinubu da Ministan kuɗi kan batun
  • A cewarsa, shugaba Tinubu zai yi jawabi kan ƙarin mafi karancin albashin a mako mai zuwa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - Shugaban Kungiyar Kwadago (TUC), Kwamared Festus Osifo, ya bayyana sakamakon ganawar da kungiyar ta yi da wakilan gwamnatin tarayya a ranar Talata.

Kungiyar ta bai wa gwamnati wa’adin makonni biyu ta magance matsalolin da ma’aikata ke fuskanta ko ta fuskanci yajin aiki saboda wahalhalun da aka shiga bayan cire tallafin man fetur.

Hoton wurin ganawar FG da NLC, TUC.
Abin Ministan Kwadago Ya Fada Mana Kan Sabon Mafi Karancin Albashi, TUC Hoto: Simon Bako Lalong
Asali: Facebook

A wata hira da aka yi da shi a Channels TV, Osifo ya ce Ministan Kwadago, Simon Bako Lalong, ya shaida musu cewa ya gana da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da Ministan Kudi, Wale Edun.

Kara karanta wannan

Gwamna da 'Yan Majalisun Tarayya Zasu Fice Daga PDP da LP Zuwa Wata Jam'iyya, Bayanai Sun Fito

Jaridar Daily Trust ta rahoto shugaban TUC na cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ministan Kwadago ya faɗa mana cewa ya tattauna da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da Ministan kuɗi, Wale Edun, kuma sun yi nazari kan batun ƙarin albashi."
"Amma shugaban ƙasa Tinubu ya umarce su da su gama gyara komai, su warware kowane batu kafin ya sanar da ci gaban a hukumance."

Zamu sa ido kan rabon kayan tallafi - TUC

Mista Osifo ya ƙara da cewa sun tattauna batun kayan tallafin da gwamnatin tarayya ta raba wa jihohi da nufin rage wa talakawa raɗaɗin halin da suka tsinci kansu.

"Za mu sanya ido kan yadda ake rarraba kayan abinci na tallafi a jihohi don tabbatar da an aiwatar da shirin yadda ya kamata. Muna son ganin jadawalin aiwatar da tsarin shi ya sa muka zauna da FG.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Shugaba Tinubu da NLC Sun Tashi Baram-Baram a Taron da Suka Yi, Bayanai Sun Fito

"Mun kuma tabo batutuwa game da haraji da Gas watau CNG. Ministan ya faɗa mana duk wadannan batutuwa za a shawo kansu amma saboda shugaban kasa ya yi tafiya mu ba shi karin mako biyu."
Muka ce masa ba zata yiwu ba, ba mu da ƙarin makonni biyu da zamu ba shi. Bayan karin tattaunawa, ya ce shugaban zai yi sanarwar da ta dace a mako mai zuwa."

Magana Ta Kare, Gwamna Obaseki Ya Aike da Wasika Ga Mataimakinsa

A wani rahoton kuma Taƙaddama kan canja wa mataimakin gwamnan jihar Edo ofis daga gidan gwamnati zuwa wani wuri ta zo ƙarshe bayan sanarwa ta fito.

Takardar sanarwan mai ɗauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar Edo, Osarodion Ogie, ta fito ne ranar Talata da safe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262