Yaron Da Aka Nemi Hanjinsa Aka Rasa Ya Kwanta Dama
- Allah ya yi wa yaron da aka nemi hanjinsa aka rasa a yayin yi masa tiyata a wani asibitin jihar Lagas rasuwa
- Adebola Akin-Bright ya kwanta dama a yammacin ranar Talata, 19 ga watan Satumba
- A ranar Talata ne majalisar dokokin Lagas ta nemi gwamnan jihar da ya sa a saki kudi domin fita da yaron waje don samun kulawar likitoci
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Rahotanni sun kawo cewa wani yaro mai suna Adebola Akin-Bright, wanda aka nemi hanjinsa aka rasa a yayin da ake masa tiyata ya mutu.
Kamar yadda jaridar The Punch ta rahoto, Akin-Bright ya mutu ne a yammacin ranar Talata, 19 ga watan Satumba.
Wata majiya ta kusa da marigayin ta fada ma jaridar cewa yaron ya samu matsala inda aka garzaya da shi sashin kula na musamman na asibitin koyarwa na jami’ar Jihar Lagas inda daga nan ne aka tabbatar da mutuwarsa.
Da farko dai majalisar dokokin jihar Lagas ta yi kira ga Gwamna Babajide Sanwo-Olu a ranar Talata kan ya umurci ma'aikatar lafiya da ta saki kudade domin a fitar da yaron kasar waje yin magani, rahoton The Nation.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Gwamnan Lagas ya ziyarci yaron da hancinsa ya bata
A ranar Lahadi, 3 ga watan Satumba ne gwamnan jihar Lagas ya ziyarci yaron a asibitin koyarwa na jami’ar Lagas da ke Ikeja, don ganin yaron wanda mahaifiyarsa, Deborah Abiodun ta yi bidiyo game da batan hanjinsa.
Mahaifiyar yaron ta bayyana cewa hanjin danta ya bata a LASUTH, cewa ta yi bidiyon ne don neman agaji.
An dai yi wa yaron tiyata a asibitoci masu zaman kansu guda biyu kafin aka mayar da shi asibitin koyarwa na jihar Lagas don gyara tiyatar, inda aka rahoto cewa hancinsa sun bata.
Babban mai ba Sanwo-Olu shawara na musamman kan kafofin sadarwa na zamani, Jubril Gawat ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.
Jigon APC ya bayyana dalilin da ya sa ya lakadawa kwamishina duka a Ondo
A wani labarin, mun ji cewa wani jigon APC a jihar Ondo, Olumide Awolumate, a ranar Talata, ya bayyana dalilin da ya sa fada ya barke tsakaninsa da kwamishiniyar harkokin mata da cigaban jama’a ta jihar, Misis Juliana Osadahun a Arigidi Akoko, Akoko ta Arewa.
A ranar Lahadi ne Awolumate da Osadahun suka ba hammata iska a wajen shirin raba kayan tallafi ga al’ummar ƙaramar hukumar, cewar rahoton Punch.
Asali: Legit.ng