An Kama Wani Mahaifi Bisa Zargin Hannu a Mutuwar Diyarsa a Nasarawa
- An tsinci gawar wata dalibar Sakandire 'yar shekara 12 a duniya a gonar mahaifinta a jihar Nasarawa
- Jami'an 'yan sanda sun kama iyayenta da suke aiki tare gabanin mutuwarta, sun sako mahaifiyar amma suna tsare da ubanta
- Wata majiya ta ce ana zargin mahaifin da yin lalata da karamar yarinyar kuma har asirinsa ya tonu
Jihar Nasarawa - An tsinci gawar matashiya yar shekara 12 a duniya, Favor Williams, da ke matakin JSS 2 a makarantar sakandire ta Kurmin Tagwaye II, karamar hukumar Akwanga a jihar Nasarawa.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa an tsinci gawar yarinyar ta wata hanya mai ban mamaki da tausayi a gonar mahaifinta.
Wani da ya shaida abin da ya faru ya ce Favor ta rataye kanta a gona a Kurmin Twagwaye II kan titin Wamba a ranatar Litinin ta makon jiya.
Sai dai wata majiya ta shaida wa wakilin jaridar cewa ana zargin mahaifin yarinyar, Mista Williams Ma’aji, da yin lalata da ita kuma asirinsa ya tonu, Daily Post ta rahoto.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Amma, shugaban matasan Kurmin Tagwaye, Thomas Vincent, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce:
"Allah ne kawai ya san abin da ya kai ga sanadin mutuwar yarinyar, wacce ba ruwanta, kuma an ganta tana harkokinta a kauyen a ranar da ta mutu."
"Mahaifin ya faɗa mana cewa Favour tana aiki a can gefen gonar tare da mahaifiyarta, bayan wani lokaci sai ya ga ta zo ta gaishe shi ta wuce wani gefen gonar, saboda ta ci gyada."
"Uban ya ce ya ɗauka ta wata hanyar ta koma wajen mahaifiyarta, amma abin mamaki da zai koma gida, sai ya ga diyarsa ta rataye kanta, kafin ya ruga ya yanke igiyar da ta yi amfani da ita, ya taras ta mutu."
Matasa sun yi yunkurin ɗaukar doka a hannu
Mista Vincenta ya kara da cewa yayin da suka isa wurin sun ga inda yarinyar ta rataye kanta, kuma matasa sun yi yunƙurin halaka iyayenta amma suka kira 'yan sanda.
"Dole ne muka shiga tsakani ta hanyar kiran ’yan sanda, suka zo suka kama su. An yi wa mahaifiyar tambayoyi aka sallame ta, amma har yanzu mahaifin na tsare.”
Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda reshen jihar Nasarawa, Nansel Ramhan, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya kara da cewa ana kan gudanar da bincike.
Kotu Ta Tsige Dan Majalisar PDP, Ta Tabbatar da Nasarar 'Yan Takarar APC 2 a Taraba
A wani rahoton kuma Jam'iyyar PDP ta ƙara rasa kujerar ɗan majalisar dokokin jihar Taraba ɗaya a gaban Kotun sauraron ƙararrakin zabe.
Haka nan kuma Kotun ta tabbatar da nasarar 'yan majalisu biyu na APC, Batulu Mohammed, mai wakiltar mazaɓar Gashaka da Abel Peter na mazaɓar Mbamnga a majalisar dokokin Taraba.
Asali: Legit.ng