Dan Majalisar Jihar Ribas, Dinebari Loolo Ya Riga Mu Gidan Gaskiya A Yau
- Iftila'i ya afkawa majalisar jihar Ribas yayin da aka sanar da wani dan majalisar jihar ya mutu a yau Litinin
- Dan majalisar, Honarabul Dinebari Loolo ya rasu a yau Litinin 18 ga watan Satumba a birnin Port Harcourt da ke jihar
- Kafin rasuwar marigayin, ya wakilci mazabar Khana 2 da ke karamar hukumar Khana da ke cikin jihar Ribas
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Ribas - Dan majalisa mai ci a jihar Ribas, Honarabul Dinebari Loolo ya riga mu gidan gaskiya a yau Litinin.
Dinebari Loolo wanda kafin rasuwar shi ya wakilci mazabar Khana 2 da ke karamar hukumar Khana a majalisar jihar ya rasu ya bar iyalai da dama.
Yaushe dan majalisar ya riga mu gidan gaskiya?
Legit ta tattaro cewa Dinebari ya mutu a Port Harcourt babban birnin jihar Ribas a yau Litinin 18 ga watan Satumba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Shugaban majalisar, Honarabul Martin Amaewhule wanda ya jagoranci sauran mambobin majalisar zuwa gidan marigayin ya bayyana Loolo a matsayin mutumin kirki.
Kakakin majalisar ya bayyana irin gudummawar da marigayin ya bayar a majalisar da kuma jihar baki daya da cewa ba za su taba mantawa da ita ba musamman a wannan lokaci.
Kakakin maalisar jihar ya kai ziyarar jaje
Martin ya bukaci iyalan marigayin da su dauki hakurin rashi inda ya ce marigayi Loolo ya kasance mai aiki tukuru ga ci gaban mazabarshi da jihar Ribas da ma kasar Najeriya baki daya
Ya yi alkwarin ci gaba da bai wa iyalan marigayi Loolo duk wata gudumawa da su ke bukata daga majalisar jihar dai-dai gwargwado a wannan lokaci.
A karshe ya yi addu'ar ubangiji ya ba su hakuri a wannan lokaci da su ke cikin wani irin mawuyacin hali inda ya musu alkawari ba su kulawa.
Majalisar Dokokin Jihar Kano Za Ta Gwangwaje Mai A-Daidaita-Sahun Da Ya Mayar Da N15m, Da Muhimmin Abu 1
Dan Majalisar Ya Rigamu Gidan Gaskiya Bayan Caka Masa Wuka
A wani labarin, wani dan majalisar dokoki a Birtaniya, David Amess, ya rasa rayuwarsa bayan wasu sun caccaka masa wuka a mazbarsa.
Rahotanni sun tabbatar cewa wasu mutane sun farmaki dan majalisar ne yayin da yake ganawa da mutanen da yake wakilta a mazabarsa.
Hakanan kuma marigayi David Amess ya kasance a majalisar dokoki a Burtaniya tun a shekarar 1983.
Asali: Legit.ng