Mutum Biyu Na Can Asibiti Jina-Jina Yayin da Gini Ya Ruguje Dasu a Wani Yankin Jihar Legas

Mutum Biyu Na Can Asibiti Jina-Jina Yayin da Gini Ya Ruguje Dasu a Wani Yankin Jihar Legas

  • An samu tsaiko a jihar Legas yayin da wani katafaren gini ya ruguje ana tsaka da zaman lafiya a cikinsa ranar Asabar
  • Ya zuwa yanzu, an ce wasu mutane da ke cikinsa suna can rai hannun Allah yayin da suka samu munanan raunuka
  • Ana yawan samun rugujewar gine-gine a Najeriya, musamman a jihar Legas da ke da gidajen sama da yawa a birnin

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Legas - Akalla mutane biyu ne ke kan gargarar rasa rayuwarsu a wani asibiti mai zaman kansa bayan da wani gini da aka mayar da shi makaranta a unguwar Ketu a jihar Legas ya ruguje a ranar Lahadi.

Ginin wanda ke dauke da dakuna sama da 800 tare da daruruwan mutane a unguwar da aka fi sani da Agboye Estate a kan titin Oduntan, Ketu, ya fara rugujewa ne a ranar Asabar da yamma sakamakon ruwan sama da aka shafe sa’o’i ana yi a Legas.

Kara karanta wannan

Rayuka Da Dama Sun Salwanta Bayan Wasu Motoci Sun Yi Taho Mu Gama

A ranar Lahadi da yamma, yayin da mazauna wurin ke ci gaba da kokarin kwashe kayansu, ginin ya sake rugujewa, inda ya lalata wani yanzi da ke harabar ginin, kafin ya ruguje gaba dayansa.

Yadda wani gini ya rushe a Legas
Gini ya danne jama'a a Legas | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Wannan lamarin ya haifar da firgici a fadin yankin, wanda ya tilastawa daruruwan ahali da mutanen da ke zaune a ginin ficewa daga harabar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda munin lamarin yake

A wata ziyarar da aka kai gidan da abin ya shafa a yammacin ranar Lahadi, an ga dimbin mazauna cikinsa na kwashe kayansu ta bangarori daban-daban yayin da jami’an hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Legas suka killace harabar ginin.

Ginin da abin ya shafa yana dauke da alamomin umarnin rushewa daga jami'an Legas da ke aiki kan ingancin gini.

A watan Disamba 2014, bayan makonni na bincike aka buga wani rahoto game da rushewar ginin da aka san da lalacewarsa.

Kara karanta wannan

Hotuna Sun Bayyana Yayin da Ambaliyar Ruwa Ta Yi Barna a Lagas, NEMA Ta Yi Martani

Yadda gini ya rushe a Abuja

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa ba da jimawa ba ginin wani Otal mai hawa hudu a yankin Dape, Life Camp, a birnin tarayya Abuja ya ruguje.

Wani shaida da abun ya faru a kan idonsa ya bayyana cewa ginin ya kife kan mutane sama da 20.

Bayanai sun nuna cewa lamarin ya faru da Misalin karfe 4:00 na yammacin ranar Litinin, 3 ga watan Yuni, 2023 yayin da ma'aikata ke tsaka da aikin gina wurin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.