Ana Zaman Zaman, Shugaba Tinubu Ya Sake Nada Sabbin Ministoci Biyu, an Fadi Sunayensu
- Shugaban kasa Bola Tinubu ya sake nadin sabbin ministoci a kasar nan, an bayyana sunayensu ga duniya
- A tun farko, an nada wasu ministoci, wadanda daga baya aka bayyana cire sunayensu saboda matsaloli
- Ya zuwa yanzu, Tinubu ya shafe kwanaki 100 a kan karagar mulki, kuma ana ci gaba da cece-kuce kan gwamnatinsa
FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya nada sabbin ministoci guda biyu da za sy kula da ma’aikatar matasa, kamar yadda rahoton Channels Tv ya bayyana.
A cewar rahoton, Tinubu ya nada Dr. Jamila Bio Ibrahim da Mista Ayodele Olawande a matsayin wadanda za su rike ma'aikatar.
A tun farko, Tinubu ya mika sunayen wasu ministoci, wadanda tuni majalisa ta amince bayan tantance su.
Waye babba kan wani?
Yayin da Jamila za ta zama babbar ministan matasa, Olawande zai zama sabon karamin minista a ma’aikatar matasa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wannan na fitowa ne daga bakin mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale ya bayyana, Tribune Online ta ruwaito.
Kafin tabbatar da wadannan ministoci, dole su je zauren majalisa domin tantance su kamar yadda dokar kasa ta tanada.
Ya aka kaya da ministocin Tinubu na farko?
Idan baku manta ba, bayan tura ministoci, an samu tsaiko a zauren majalisa yayin tantance wasu daga cikinsu.
Daga ciki, majalisar ta bayyana shakku tare da bayyana korafi kan tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai.
Ya zuwa wancan lokacin, majalisar bata amince da mutum uku ba daga cikin wadanda Tinubu ya nada.
Duk da haka, an tabbatar da wasu daga ciki, tare da ba su ma'aikatun da za su rike domin ci gaba da yiwa kasar hidima.
Bukatar wata kungiya ga Tinubu
An bukaci ministocin Shugaba Tinubu da su yi murabus idan har sun san ba za su iya taimakawa ba wajen cimma ajandar gwamnatin nan ba ta "Renewed Hope".
Kungiyar wasu masu kishin dimokuraDiyya mai suna The Natives, ita ce ta yi wannna kiran a ranar Laraba, 23 ga watan Agusta a birnin tarayya Abuja, yayin ganawa da manema labarai.
Da yake magana a wajen, shugaban Kungiyar, Hon, Smart Edwards, ya bukaci ministocin da su yi koyi da irin halin shugabanci nagari na Shugaba Tinubu, ko su rasa muƙamansu.
Asali: Legit.ng