Obasanjo Na Gab Da Rasa Sarautarsa, An Ba Shi Wa’adi Ya Bai Wa Sarakunan Oyo Hakuri

Obasanjo Na Gab Da Rasa Sarautarsa, An Ba Shi Wa’adi Ya Bai Wa Sarakunan Oyo Hakuri

  • An bukaci sarakunan gargajiya a kasar Yarbawa da su hada kai sannan su tubewa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo duk rawani na duk sarautan da yake da su'
  • Hakan ya biyo bayan yar dirama da ta wakana tsakanin tsohon shugaban kasar da wasu sarakunan gargajiya a jihar Oyo
  • Shugaban majalisar Yarbawa ta duniya, Aare Oba Oladotun Hassan, Esq, ya nemi a janye sarautar Obasanjo

FCT, Abuja - Majalisar Yarbawa ta duniya ta bai wa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo wa'adin kwana uku ya bai wa sarakunan Oyo da suka halarci bikin haddamar da hanyar Oyo-Iseyin a ranar Juma'a, 15 ga watan Satumba hakuri.

Obasanjo ya sha suka a shafukan midiya bayan an gano shi a cikin wani bidiyo da ya yadu yana cin mutuncin sarakuna saboda basu mike tsaye ba a lokacin da tsohon shugaban kasar ya halarci wani taro.

Kara karanta wannan

Yan Soshiyal Midiya Sun Taso Obasanjo a Gaba Bayan Ya Yi Wa Sarakuna Wani Abu 1 a Bainar Jama'a

An nemi Obasanjo ya ba sarakunan Oyo hakuri
Obasanjo Na Gab Da Rasa Sarautarsa, An Ba Shi Wa’adi Ya Bai Wa Sarakunan Oyo Hakuri Hoto: @Oolusegun_obj/@tvcnewsng
Asali: Twitter

Da yake hira ta musamman da Legit a kan wannan lamari, shugaban majalisar Yarabawa ta duniya, Aare Oba Oladotun Hassan, Esq, ya bayyana abun da Obasanjo ya yi a matsayin rashin da'a.

Ya ce abin da Obasanjo ya yi yaudara ne da cin mutuncin al’adun Yarabawa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce:

"A matsayina na shugaban Majalisar Yarbawa ta duniya, mun fito fili mun yi Allah wadai da wannan dabi'a da zubar kimar al'adunmu, wanda ya fi kunyata mutunci da kimar al'adunmu.
"Mun san cikin abun da Cif Olusegun Obasanjo ya fado. Watakila ya fadi ne don ya nuna jin kansa. Amma mu a wajenmu, ba za mu dauke shi a haka ba, muna neman ya ba da hakuri a taron manema labarai cikin kwanaki uku masu zuwa kama daga jiya da ya aikata laifin."

Kara karanta wannan

Shugabannin Yarabawa sun yi taro a Legas, sun aikawa Bola Tinubu Sako zuwa Abuja

Obasanjo ya aika sakon da bai dace ba ga sarakunan Yarbawa

Aare Hassan ya bayyana cewa abun da Obasanjo ya yi ya aika sako da bai dace ba ga dukkan sarakuna a kasar Yarbawa.

Ya bukaci daukacin sarakuna a kasar Yarbawa su hadu sannan su fara daukar matakai don karfafa majalisar gargajiya a yankin.

Za a tubewa Obasanjo sarautarsa

Ya bayyana cewa idan har Obasanjo ya ki yin abun da ya kamata, a tube masa dukkan sarautar da yake da su a kasar Yarbawa.

Aare Hassan ya ce za a dauki duk sarkin da bai tubewa Obasanjo rawaninsa ba a matsayin maci amana a kasar Yarbawa.

Ya kuma bayyana cewa ya kamata Obasanjo ya gane cewa yanzu shi ba shugaban kasar Najeriya bane.

Obasanjo ya umarci sarakuna su mike su gaida shi a wajen wani taro a jihar Oyo

A baya mun kawo cewa tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya sami kansa a cikin wani cece-kuce bayan wani abu da ya yi a wajen ƙaddamar da titin hanyar Iseyin-Oyo mai tsawom kilomita 34.85 a a ranar, Juma'a 15 ga watan Satumban 2023.

Obasanjo wanda gwamna Seyi Makinde ya gayyato, an kuma ba shi damar ƙaddamar da sabuwar harabar jami'ar fasaha ta Ladoke Akintola (LAUTECH) a Isiyen, wacce ke ɗauke da kwalejin noma da sabunta albarkatun ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

iiq_pixel