Tinubu Ya Nada Muri-Okunola, Yakasai, Da Wasu 14 a Matsayin Hadimansa
- Shugaban ma'aikatan jihar Lagas mai ci, Hakeem Muri-Okunola, shine babban sakataren shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
- Lauyan mai shekaru 51 zai koma yi wa Tinubu aiki karo na farko bayan ya nada shi a matsayin mai taimaka masa na musamman a 2001 lokacin da yake matsayin gwamna
- Shugaban kasa Tinubu ya nada wasu hadimai na musamman guda 15, wadanda suka hada da Tanko Yakasai, Adejoke Orelope-Adefulire, da Moremi Ojudu
FCT, Abuja - Rahotanni da ke zuwa sun tabbatar da nada shugaban ma'aikatan jihar Lagas, Hakeem Muri-Okunola, a matsayin babban sakataren shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
An nada Muri-Okunola tare da wasu mutane 15 da suka hada da Tanko Yakasai, Adejoke Orelope-Adefulire, da Moremi Ojudu, PM News ta rahoto.
Takaitaccen bayanin Muri-okunola kafin nadin shugaban kasa
Lauyan mai shekaru 51 ya fara aiki da shugaban kasa Tinubu lokacin da yake matsayin gwamnan jihar Lagas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tattaro cewa Muri-Okunola ya yi aiki a matsayin hadimin Tinubu na musamman a lokacin da yake matsayin gwamna.
Ya fara aiki da gwamnatin jihar Lagas tun a farkon shekarun 2000s, lokacin da ya yi aiki a matsayin babban sakataren kwamitin amfani da filaye, akatare na dindindin sannan kuma daga bisani shugaban ma’aikata.
An nada Moremi Ojudu, diyar Babafemi Ojudu, tsohon mai ba tsohon mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo na shawara ta musamman kan harkokin labarai, a matsayin mai ba shugaban kasar shawara ta musamman kan harkokin al’umma a yankin kudu maso yamma.
Hakazalika an nada Tanko Yakasai, Chioma Nweze, Abiodun Essiet, da Abdulhamid Yahaya Abba mukamai don yin aiki a sauran yankuna biyar.
Yakasai ai kasance na areewa maso yamma, Essiet arewa ta tsakiya, Nweze kudu maso gabas, Yahaya Abba arewa maso gabas.
Nadin ya kuma nuna cewa an sake nada tsohuwar mataimakiyar gwamnan Lagas, Adejoke Orelope Adefulire a matsayin mai ba da shawara ta musamman kan Manufofin Ci Gaba Mai Dorewa.
Tinubu Ya Dauko ‘Dan Takaran Shugaban Kasa, Ya Ba Shi Mukami a Gwamnatinsa
A wani labarin, mun ji cewa Shugaban kamfanin Global Analytics Consulting Limited, Tope Fasua ya samu mukami a gwamnati mai-ci a Najeriya.
Mista Tope Fasua ya yi magana a shafin X wanda aka fi sani da Twitter, ya ce ya zama mai bada shawara ga gwamnatin tarayya.
Asali: Legit.ng