An Ceto Mutum 33 Da Yan Bindiga Suka Sace a Jihar Bauchi
- Jami'an tsaro sun samu nasarar kuɓutar da mutum 33 da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Bauchi
- Jami'an tsaron sun ceto mutanen ne bayan sun yi artabu da miyagun ƴan bindigan a ƙaramar hukumar Alkaleri ta jihar
- An samu nasarar ceto su ne kwana ɗaya bayan ƴan bindigan sun yi awon gaba da su zuwa cikin daji
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Bauchi - Aƙalla mutane 33 da aka yi garkuwa da su, waɗanda suka haɗa da mata da ƙananan yara ne suka samu ƴanci sa’o’i 24 bayan an yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Alkaleri ta jihar Bauchi.
An ceto mutanen da lamarin ya ritsa da su ne biyo bayan umarnin da gwamnan jihar Bala Mohammed Abdulkadir, wanda ya fito daga yankin ya bayar, cewar rahoton Daily Trust.
Yan Sanda Sun Samu Gagarumar Nasarar Cafke Wani Ƙasurgumin Dan Bindigan Da Aka Dade Ana Nema a Jihar Arewa
An samu labarin cewa rundunar haɗin gwiwa ta jami’an tsaro ne ta yi artabu da ƴan ta’addan, inda ta samu nasarar kuɓutar da dukkan mutum 33 da aka yi garkuwa da su.
An miƙa mutanen hannun hukumomi
Shugaban riko na ƙaramar hukumar Alkaleri, Kwamared Bala Ibrahim Mahmoud ya karɓi wadanda abin ya shafa a daren Juma’a, 15 ga watan Satumba, daga hannun jami’an tsaro a Yalwan Duguri cikin ƙaramar hukumar Alkaleri.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mahmoud ya ce wasu ƴan bindiga ne suka yi garkuwa da mutanen a kan hanyarsu ta dawowa daga kasuwa sannan suka tafi da su zuwa cikin daji.
Mahmoud ya yabawa jami’an tsaron bisa matakin gaggawa da suka ɗauka wanda a ƙarshe ya kai ga sakin mutanen da aka yi garkuwa da su
Ya yi alkawarin cewa dukkan mutanen 33 da aka sako waɗanda aka sace, sai an tabbatar da an duba lafiyarsu kafin ɗaukar wani mataki na gaba.
Da Dumi-Dumi: Rayuka Da Dama Sun Salwanta Bayan Yan Bindiga Sun Kai Wani Sabon Hari a Arewacin Najeriya
Ƙaramar hukumar Alkaleri dai na ɗaya daga cikin ƙananan hukumomi uku na jihar Bauchi inda ƴan fashi da makami ke ke cin karensu ba babbaka, suna garkuwa da mutane yadda suka ga dama tare da karɓar maƙudan kudaden fansa daga iyalan wadanda lamarin ya shafa.
Yan Bindiga Sun Halaka Mutane a Kaduna
A wani labarin kuma, miyagun ƴan bindiga sun halaka mutum biyu a wani sabon hari da suka kai a ƙauyen Dogon Noma-Unguwan da ke ƙaramar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.
Miyagun ƴan bindigan bayan sun kashe aƙalla rayuka biyu, sun kuma yi awon gaba da wasu mutun uku zuwa cikin daji.
Asali: Legit.ng