UAE Ta Musanta Cire Takunkumin Ba Yan Najeriya Biza

UAE Ta Musanta Cire Takunkumin Ba Yan Najeriya Biza

  • Sabbin bayanai sun fito dangane da batun dakatar da ba ƴan Najeriya biza da ƙasar haɗaɗɗiyar daular Larabawa (UAE) ta yi
  • Wani jami'in gwamnatin UAE ya bayyana cewa ƙasar ba ta cire umarnin dakatar da ba matafiya ƴan Najeriya biza ba
  • Majiyar wanda ya nemi kada a bayyana sunansa ya bayyana cewa har yanzu babu abin da ya sauya dangane batun dakatar da bizar

Wani jami'in gwamnatin ƙasar hadaɗɗiyar daular Larabawa (UAE), ya musanta batun cewa ƙasar ta cire takunkumin bayar da takardar biza da ta ƙaƙaba akan matafiya ƴan Najeriya.

A cewar rahoton CNN, majiyar wanda ya nemi kada a bayyana sunansa, ya bayyana hakan ne a cikin wata tattaunawa.

UAE ta musanta cire takunkumin ba yan Najeriya biza
UAE ta musanta batun cire takunkumin ba yan Najeriya biza Hoto: @NGRPresident
Asali: Twitter

UAE ba ta cire takunkumin biza kan ƴan Najeriya ba

Jami'in gwamnatin na UAE ya bayyana cewa:

Kara karanta wannan

Bola Tinubu, Ganduje da Manyan Hafsoshin Tsaro Sun Yi Kus-Kus Kan Abu 1 a Villa, Ƙarin Bayani Ya Fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Har yanzu babu wani sauyi dangane da matsayar tafiye-tafiye tsakanin Najeriya da UAE."

Majiyar ya buƙaci kada a bayyana sunansa saboda baya da hurumin yin magana da kafafen watsa labarai.

UAE a cikin wata sanatwa a watan Oktoban shekarar da ta gabata ta bayyana cewa ta dakatar da bayar da takardar biza ga ƴan Najeriya da wasu ƙasashen Afirika guda 19. Ƙasar ba ta kuma bayar da ƙarin bayanai.

An kuma dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a tsakanin ƙasashen biyu bayan kamfanin jirgin Emirates ya tsayar da ayyukansa bisa dalilin an riƙe masa kuɗaɗensa a Najeriya.

Nasarorin ziyarar Tinubu a UAE

Sanarwa ta fito daga fadar shugaban kasar cewa an kawo karshen takunkumin da aka kakabawa ‘yan Najeriya zuwa UAE.

A ranar Litinin, Mai girma Bola Ahmed Tinubu da shugaban UAE, Mohamed bin Zayed Al Nahyan su ka cin ma matsaya a zaman da su ka yi.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya Ta Ba Mambobin Majalisar Wakilai Tallafin N100m? Gaskiya Ta Fito Filii

Mai taimakawa shugaban Najeriyan wajen yada labarai da hulda da jama’a, Ajuri Ngelale ya fitar da wannan sanarwa.

Gwamnati Ta Yi Magana Biyu Ƙan Jiragen Emirates

A wani labarin kuma, gwamnatin tarayya ta yi amai ta lashe inda ta ce babu wani lokaci da aka tsaida domin jiragen sama su cigaba da jigilar daga Najeriya zuwa UAE.

Gwamnatin tarayyar ta bayyana cewa cigaba da aikin kamfanonin Emirates da Etihad ba zai zama da wuri kamar yadda aka fada ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng