Kamfanin Samar Da Wutar Lantarki Na Jihar Kebbi Ya Kama Da Wuta

Kamfanin Samar Da Wutar Lantarki Na Jihar Kebbi Ya Kama Da Wuta

  • Gobarar tsakar dare ta kama a kamfanin samar da wutar lantarki na Najeriya (TCN) da ke Birnin Kebbi
  • Lamarin ya haddasa rudani a tsakanin mazauna kauyen Mechanic da ke Birnin Kebbi
  • Legit.ng ta gano bidiyoyi a soshiyal midiya wanda ke nuna yadda gobarar ta shafi manyan kayan aiki na kamfanin raba wutar

Birnin Kebbi, Jihar Kebbi - Kwana daya bayan gobara ta tashi a tashar wutar lantarki na Kainji da ke jihar Neja wanda ya yi sanadiyar daukewar wuta a fadin kasar, kamfanin samar da wutar lantarki na Najeriya (TCN) da ke jihar Kebbi ya kama da wuta.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, har yanzu ba a san musababbin tashin gobarar ba.

Wuta ya kama a kamfanin rarraba wutar lantarki na Kebbi
Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki Na Jihar Kebbi Ya Kama Da Wuta Hoto: @BayoAdelabu
Asali: Twitter

Gobara ta tashi a kamfanin samar da wutar lantarki na Kebbi

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Wutar Lantarki A Najeriya Ta Dawo Bayan Shafe Sa'o'i Babu Ita, An Bayyana Dalilin Hakan

Wasu mazauna yankin da kamfanin yake a bayan Mechanic Village da ke garin Birnin Kebbi sun ce sun ji karar fashewar abu sai kuma wuta da hayaki ya biyo baya daga wani sashi na kamfanin samar da wutar da misalin karfe 12:32 na dare.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Deeni Jibo, mai daukar hoton mataimakin gwamnan jihar Kebbi, ya ce bai taba ganin irin haka ba a rayuwarsa. Ya roki Allah ya kare wadanda ke cikin garin.

Kamfanin samar da wutar lantarkin shine ke raba wuta zuwa Kebbi, Sokoto da Zamfara da kuma Jamhuriyar Nijar, kamar yadda jaridar Nigerian Tribune ta rahoto.

wanda shi ne mai daukar hoto na rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin. Sai dai ya ce har yanzu bai samu cikakken bayani kan lamarin ba.

Kara karanta wannan

Rikita-rikita Yayin Da Ake Shirin Mika Yankin Adamawa Ga Kamaru, An Bayyana Dalili

Bayan daukar lokaci, an sake dauke wutar lantarki a fadin Najeriya baki daya

A halin da ake ciki, Legit Hausa ta rahoto a baya cewa an dauke wutar lantarki gaba daya a fadin Najeriya.

Lamarin ya faru ne da safiyar ranar Alhamis 14 ga watan Satumba a gaba daya fadin kasar.

Hakan ya faru ne makonni kadan da Kamfanin Samar da Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya cika shekara daya ba tare da an samu daukewar wutar gaba daya ba a kasar.

Sai dai kuma daga bisani Kamfanin Samar da Wutar Lantarki a Najeriya (TRCN) ta sanar da gyara wutar lantarki da ta baci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng