Matsalar Tsaro: Abinda Ya Sa Iyaye Ke Fargabar Tura 'Ya'yansu Makaranta, Ministan Tinubu
- Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa iyaye na tsoron tura 'ya'yansu makaranta ne saboda tsoron harin yan bindiga
- Ministan harkokin cikin gida, Tunji-Ojo ya ce yawan hare-haren da ake kaiwa makarantu tun 2014 babban abin damuwa ne
- Gwamnan jihar Benuwai ta tabbatar da cewa gwamnatinsa zata bada goyon baya a shirin samar da aminci a makarantun jihar
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT Abuja - Ministan harkokin cikin gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ya ce a yanzu iyaye na tsoron tura 'ya'yansu makaranta saboda matsalar tsaron da ta damu ƙasar nan.
Tunji-Ojo ya faɗi haka ne a sakonsa na fatan alheri da ya gabatar a wajen taron kaddamar da tsarin “Samar da tsaro a makarantu” da aka gudanar a Makurdi, babban birnin jihar Benuwai.
Ya ce, "Iyaye suna tsoron tura 'ya'yansu makaranta saboda tsoron kai hare-haren 'yan ta'adda."
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Ministan ya yi jawabi ne ta bakin kwamandan rundunar jami'an Sibil Difens (NSCDC), Ahmed Abubakar Audi, wanda ya wakilce shi a wurin taron.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ministan ya jaddada cewa taɓarɓarewar tsaro da yawan kai hari makarantun ƙasar nan tun 2014 irin wanda aka sace ɗaruruwan ɗalibai mata a Chibok, ba ƙaramin abun damuwa bane.
Sai dai a nasa jawabin a wurin bikin yaye jami'ai 364 da aka ba horon samar da tsaro a makarantun Benuwai da sauran jihohi, Mista Audi ya yaba da tsarin tsaro a makarantu.
Wane nasarori sabon tsarin tabbatar da tsaro a makarantun ya samu?
Ya bayyana cewa zuwa yanzu shirin ya daƙile kai hare-hare sama da 30 a makarantun fadin kasar, tun bayan da aka fara aiwatar da shi a Najeriya, rahoton Trust Radio.
Gwamna Hyacinth Alia, a jawabinsa na musamman a wajen bikin, ya yi alkawarin goyon baya daga gwamnatinsa wajen ba da fifiko kan harkokin tsaro a makarantu, inda ya jaddada muhimmiyar rawar da ilimi ke takawa wajen ci gaba.
Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Ganduje da Hafsoshin Tsaro a Villa
A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya gana da shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, da manyan hafsoshin tsaro a Aso Villa.
Wakilan ƙungiyar fulani makiyaya ta ƙasa MACBAN sun halarci zaman wanda ya maida hankali kan muhimmin batu.
Asali: Legit.ng