Hawaye Sun Kwaranya Yayin da Yan Bindiga Suka Fille Kan Daraktan Kamfen Din Labour Party a Abia

Hawaye Sun Kwaranya Yayin da Yan Bindiga Suka Fille Kan Daraktan Kamfen Din Labour Party a Abia

  • An kashe jigon jam'iyyar Labour Party a jihar Abia, Maduka Zachary, wanda aka fi sani da "Power Zac"
  • An rahoto cewa wasu da ba a san ko su waye ba ne suka fille kan Power Zac a mahaifarsa ta Uturu inda suka tafi da kan nasa
  • Ya kasance daraktan kamfen din jam'iyyar a karamar hukumar Uturu kuma daraktan kamfen din Hon. Abobi Ogah a zaben 2023

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Umuahia, Abia - Rahotanni sun kawo cewa miyagu sun fille kan wani jigon jam'iyyar Labour Party a jihar Abia, Maduka Zachary, wanda aka fi sani da "Power Zac".

Kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto, Power Zac ya kasnace daraktan kamfen din jam'iyyar Labour Party a Uturu, karamar hukumar Isuikwuato da ke jihar a zaben 2023.

Kara karanta wannan

An Bar Najeriya Babu Kowa, Tinubu da Kashim Shettima Duk Sun Tafi Kasar Waje

Wasu miyagu sun fille kan wani jigon LP a jihar Abia
Hawaye Sun Kwaranya Yayin da Yan Bindiga Suka Fille Kan Daraktan Kamfen Din Labour Party a Abia Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Twitter

An kashe daraktan kamfen din Amobi Ogah a Abia

Marigayin ya kuma kasance daraktan kamfen din Hon. Amobi Ogah, dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Isuikwuato/Umunneochi a majalisar wakilai.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bugu da kari, shine shugaban reshe na kungiyar Uturu.

Kamar yadda rahotanni suka kawo, wasu miyagu da ba a san ko su waye bane suka kashe jigon na Labour Party a mahaifarsa da ke Uturu, inda suka yi awon gaba da kansa.

An kuma rahoto cewa yana daga cikin tawagar jami'an tsaro na yankin da ke yaki da rashin tsaro a garin Uturu.

Rundunar yan sanda ta magantu a kan kisan jigon Labour Party a Abia

Da aka tuntube ta don tabbatar da lamarin, Maureen Chinaka, kakakin yan sandan jihar Abia ta ce bata samu jawabi kan lamarin ba tukuna, rahoton The Guardian.

Kara karanta wannan

EFCC ta Cafke Mutumin Jonathan da Orubebe, An Yanke Masu Daurin Shekaru 6

Ta yi alkawarin yin jawabi ga manema labarai idan ta samu bayani game da al'amarin.

Jawabinta:

"Ba a sanar da ni ba tukuna. Bani da labari a yanzu dangane da hakan. Don haka zan tuntube ku idan aka sanar da ni."

Jam'iyyar Labour Party reshen Abia ta tabbatar da mutuwar babban jigonta

A halin da ake ciki, shugaban jam'iyyar Labour Party a jihar Abia, Ceekay Igara ya tabbatar da lamarin.

Ya ce shugaban jam'iyyar a karamar hukumar ya tabbatar masa da faruwar lamarin lokacin da suka yi magana.

Sojoji sun kama makashin Dorathy Jonathan a kudancin Kaduna

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta rahoto a baya cewa dakarun Operations Safe Haven sun kama wani matashi mai suna Lot Dauda, wanda ya kashe Dorathy Jonathan a kudancin jihar Kaduna.

An kashe matashiyar yayin da ta je debo itatuwa a kauyen Afana da ke karamar hukumar Zango Kataf a jihar a ranar Juma'a, 1 ga watan Satumba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng