Bayan Daukar Lokaci, An Sake Dauke Wutar Lantarki A Fadin Najeriya Baki Daya

Bayan Daukar Lokaci, An Sake Dauke Wutar Lantarki A Fadin Najeriya Baki Daya

  • Bayan daukar lokaci mai tsawo, a safiyar yau Alhamis an sake dauke wuta a fadin Najeriya gaba daya
  • Wannan na zuwa ne bayan cika shekara guda ba tare da samun wannan matsalar ba a kasar sakamakon lalacewarta
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa matsalar daukewar wutar ta fara ne da misalin karfe 12:40 na dare

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Rahotanni sun tabbatar da cewa an dauke wutar lantarki gaba daya a fadin Najeriya.

Lamarin ya faru ne da safiyar yau Alhamis 14 ga watan Satumba a gaba daya fadin kasar, Legit ta tattaro.

An dauke wuta gaba daya a Najeriya
An Sake Dauke Wutar Lantarki A Fadin Najeriya Baki Daya. Hoto: The Glitters, Heritage Times.
Asali: UGC

Me ya jawo daukewar wutar a Najeriya?

Wannan na zuwa ne makonni kadan da Kamfanin Samar da Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya cika shekara guda ba tare daukewar wutar gaba daya ba a kasar.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Wutar Lantarki A Najeriya Ta Dawo Bayan Shafe Sa'o'i Babu Ita, An Bayyana Dalilin Hakan

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cikin wata sanarwa da kamfanin rarraba wutar lantarki na Enugu ya fitar, ya ce wutar ta fara daukewa ne da misalin karfe 12:40 na daren yau.

Daily Trust ta tattaro cewa karfin wutar lantarki a Najeriya ya ragu zuwa megawatt 273 a kasar.

A cikin wata sanarwa da kamfanin samar da wutar lantarki a jihar Enugu (EEDC) ya sanar da haka inda ya ce yanzu haka ba sa iya samar da wutar a bangarori da yawa.

Meye hukumar wuta ta ce kan daukewar wutar?

Sanarwar ta ce:

"Saboda samun matsalar da wutar ta yi, duk wuraren samar da wutar ba za su iya samar da ita ba.
"Ba za mu iya samar da wutar ba ga kwastomominmu da ke jihohin Enugu da Imo da Abia da Ebonyi da kuma Anambra."

Kara karanta wannan

EFCC ta Cafke Mutumin Jonathan da Orubebe, An Yanke Masu Daurin Shekaru 6

Wannan shi ne karon farko da aka samu irin haka tun bayan hawan shugaban kasa, Bola Tinubu kan mulki.

A lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari an samu irin wannan matsalar a lokuta da dama.

An dawo da wuta a Najeriya

A wani labarin, Kamfanin Samar da Wutar Lantarki a Najeriya (TRCN) ta sanar da gyara wutar lantarki da ta baci a yau Alhamis.

An wayi garin yau Alhamis 14 ga watan Satumba babu wuta a gaba daya Najeriya wanda shi ne karon farko cikin shekara daya kamar yadda kamfanin ya sanar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.