Majalisar Wakilai Ta Musanta Batun FG Ta Ba Mambobinta Tallafin N100m
- Majalisar wakilai ta fito fili ta musanta batun cewa gwamnatin tarayya ta cika aljihun mambobinta da N100m a matsayin tallafi
- Mataimakin sakataren ƙungiyar NLC, Mista Christopher Onyeka, shi ne ya fito ya yi wannan zargin a cikin wata sanarwa
- Majalisar wakilan ta bayyana zargin a matsayin mara tushe ballantana makama, inda ta ce ko kaɗan mambobinta ba su samu waɗannan kuɗaɗen ba
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Majalisar wakilai ta musanta batun da ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC), ta yi na cewa gwamnatin tarayya ta ba mambobinta N100m a matsayin tallafi, cewar rahoton The Punch.
Mataimakin sakataren ƙungiyar NLC na ƙasa, Christopher Onyeka, shi ne ya yi zargin a wata sanarwa a birnin tarayya Abuja.
Da yake martani kan zargin, shugaban kwamitin watsa labarai da hulɗa da jama'a na majalisar, Akin Rotimi, ya bayyana zargin a matsayin mara tushe ballantana makama.
Shugaban kwamitin ya musanta karɓar kuɗin ne a cikin wata sanarwa da ya fitar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Majalisa ta musanta samun tallafi daga FG
Wani ɓangare na sanarwar na cewa:
"Majalisar wakilai ta lura cike da takaici rahotannin da ke yawo a jaridu da kafafen sada zumunta kan wata sanarwa da aka jingina ta akan mataimakin sakataren ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa, Mista Christopher Onyeka."
"Da farko dai, muna bayyana cewa Mista Onyeka ya tafka ƙarya a iƙirarin da ya yi na cewa gwamnatin tarayya ta ba ƴan majalisa N100m a matsayin tallafi."
"Ɗomin kawar da kowane irin shakku, ƴan majalisu ba su taɓa amsar wasu kuɗi daga hannun ɓangaren zartaswa ba a matsayin tallafi. Saboda haka, muna kallon wannan sanarwar a matsayin wacce ba ta dace ba."
"Muna ganin ta a matsayin ba ta dace ba kuma abin takaici ne a ce Mista Onyeka zai yi ƙarya a wani yunkuri na neman amincewa da wasu bukatu na NLC yayin da yake neman tozarta majalisa da kuma tunzura jama’a dangane da ita."
Majalisa ta buƙaci NLC ta nemi afuwa
Majalisar wakilan ta kuma buƙaci ƙungiyar ta janye wannan ƙaryar da ta yi mata sannan ta fito fili ta nemi afuwa, rahoton The Cable ya tabbatar.
"Muna son mu tunatar da NLC da dukkanin ƴan Najeriya cewa a cikin ƙasa da kwana 100 na wannan majalisa ta 10, mun nuna jajircewarmu kan jindaɗin ma'aikata a ƙasar nan da dukkanin ƴan Najeriya."
Buhari Ya Koma Gona
A wani labarin kuma, kun ji cewa Malam Garba Shehu, kakakin toshon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa tsohon shugaban ƙasan ya rungumi noma hannu bibbiyu.
Garba Shehu ya bayyana cewa Buhari yana gonarsa ta Daura domin ba ta cikakkiyar kulawa saboda ba ta samu hakan ba a lokacin da baya nan.
Asali: Legit.ng