Gwamnan Jihar Akwa Ibom Ya Sanya Dokar Kulle a Wasu Kauyuka 4 Na Jihar
- Gwamnan jihar Cross Rivers ya sanya dokar kulle a wasu ƙauyuka huɗu na ƙaramar hukumar Yaba ta jihar
- Gwamna Bassey Otu ya sanya dokar kullen ne biyo bayan rikicin da y ɓarke kan filaye da iyakoki a ƙauyukan
- Kakakin gwamna Otu shi ne ya sanar da sanya dokar kullen a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, 12 ga watan Satumba
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Cross Rivers - Gwamna Bassey Otu na jihar Cross Rivers a ranar Talata ya sanya dokar kulle a ƙauyukan Ugaga, Igbekurekor, Benekaba da Ijama na ƙaramar hukumar Yala ta jihar.
Gwamnan ya sanya dokar kullen ne bayan an samu ɓarkewar rikici a ƙauyukan, cewar rahoton PM News.
Rikicin filaye da iyakoki a tsakanin ƙauyukan guda huɗu ya jawo matsalar rashin tsaro a yankin wacce ta haifar da asarar rayuka da dukiyoyi.
A cewar gwamnan, an sanya dokar kullen ne domin hana cigaba da aukuwar rikicin da kuma ba jami'an tsaro damar shawo kan matsalar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Hakan dai na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin gwamna Otu, Mista Emmanuel Emmanuel Ogbeche, ya fitar a ranar Talata, 12 ga watan Satumba, a birnin Calabar, babban birnin jihar.
Dalilin gwamna Otu na sanya dokar kullen
Wani ɓangare na sanarwar na cewa:
"Dokar kullen ta zama wajibi biyo bayan rikicin kan iyaka da ke haifar da barazanar tsaro wacce ta haifar da asarar rayuka da dukiyoyin jama'a"
"Don haka na sanya dokar kulle a ƙauyukan Ugaga da Igbekurekor na ƙaramar hukumar Yaba, da ƙauyukan Benekaba da Ujama."
Otu ya umarci hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar da ta samar da shirin gaggawa na kayan agaji ga mutanen da rikicin ya ritsa da su, rahoton Premium Times ya tabbatar.
Gwamnan ya ja kunnen sarakunan gargajiya
Ya buƙaci sarakunan gargajiya na ƙauyukan da su gaggauta samar da hanyoyin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Gwamnan ya bayyana cewa zai ɗora musu alhakin duk wani rashin bin doka da oda da ya sake aukuwa a yankunansu.
Ya kuma buƙaci al'ummar ƙauyukan da abin ya shafa da su haƙura da rikicin su zauna lafiya da junansu.
Rikici Ya Barke Tsakanin Mambobin NURTW
A wani labarin kuma, mambobin ƙungiyar direbobin motocin sufuri ta ƙasa (NURTW) sun ba hammata iska a birnin tarayya Abuja.
Mambobin ƙungiyar masu biyayya ga shugaban ƙungiyar, Tajudeen Baruwa da magoya bayan Badru Agbese ne suka yi rikicin wanda har bindigu aka harba.
Asali: Legit.ng