Jerin Ministocin Tinubu Da Kotu Ta Ayyana a Matsayin Wadanda Suka Lashe Zaben Majalisun Tarayya

Jerin Ministocin Tinubu Da Kotu Ta Ayyana a Matsayin Wadanda Suka Lashe Zaben Majalisun Tarayya

Zuwa yanzu, biyu daga cikin ministocin shugaban kasa Bola Tinubu sun yi nasara a korafe-korafen da suka shigar kotun sauraron kararrakin yan majalisun tarayya.

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Ministocin biyu sune tsohon gwamnan jihar Filato, Simon Lalong da Nkeiruka Onyejeocha.

Ministocin Bola Tinubu biyu sun yi nasara a karar da suka shigar kotun zabe
Jerin Ministocin Tinubu Da Kotu Ta Ayyana a Matsayin Wadanda Suka Lashe Zaben Majalisun Tarayya Hoto: @nkeiruka_reps, @LalongBako
Asali: Twitter

Simon Lalong

Lalong na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya yi takarar kujerar sanata mai wakiltan Filato ta kudu sannan ya sha kaye a hannun Napoleon Bali na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Bayen kayan da ya sha, sai shugaban kasa Tinubu ya nada shi a matsayin ministan kwadago da daukar ma'aikata.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai kuma, a ranar Litinin, 11 ga watan Satumba, kotun zabe da ke zama a Jos ta ayyana Lalong a matsayin wanda ya lashe zaben sannan ta tsige Sanata Bali daga kujerarsa.

Kara karanta wannan

Kotun Zabe Ta Tsige Dan Majalisar Tarayya Na NNPP, Ta Bai Wa Jam'iyyar APC Nasara a Jihar Arewa

Kotun zaben karkashin jagorancin Mai shari'a Omaka Elekwo ta soke zaben Bali saboda gazawar PDP wajen mutunta umarnin da wata babbar kotun Jos ta bayar na gudanar da taron gundumomi kafin zaben da ya gabata.

Nkeiruka Onyejeocha

Onyejeocha, ta jam'iyyar APC ma ta yi takarar kujerar yar majalisa mai wakiltan mazabar Isuikwuato/Umunneochi a majalisar wakilai sannan ta sha kaye a hannun Amobi Ogah na jam'iyyar Labour Party (LP), kamar yadda sakamakon INEC ya nuna.

Bayan kayen da ta sha, shugaban kasa Tinubu ya nada Onyejeocha a matsayin karamar ministar kwadago da daukar ma'aikata.

Sai dai kuma, kotun zabe da ke zama a Umuahia ta tsige Ogah a ranar Laraba, 6 ga watan Satumba.

Haka kuma kotun ta umurci hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) da ta janye takardar shaidar cin zabe da ta bai wa Ogah sannan ta bayar da shi ga wacce ke kara, Onyejeocha.

Kara karanta wannan

Ahaf: Rashin Gaskiya Ta Sa Kotu Ta Tsige Dan Majalisar NNPP a Kano, An Ba Dan Takarar APC

Shin Lalong da Onyejeocha za su bar majalisar Tinubu?

Koda dai kotun zaben ta ayyana Lalong da Onyejeocha a matsayin wadanda suka lashe zabe, abokan hamayyarsu na da damar daukaka kara kan hukuncin, matakin da akwai yiwuwar shi za su dauka.

Sai dai kuma, idan ministocin biyu suka yi nasara a kotun Allah ya isa, ya rage a san ko za su bar majalisar Shugaban kasa Tinubu zuwa majalisar dokokin tarayya ko ba za su bari ba.

Yayin da Lalong ya nuna farin ciki da nasarar da ya samu a kotun zabe, tsohon gwamnan ya yi shiru game da mataki na gaba da zai dauka.

Onyejeocha, wacce ta yi martani ga nasararta, bata bayyana mataki na gaba da take shirin dauka ba idan ta yi nasara a kotun karshe.

Kotun zabe ta kwace kujerar dan majalisar tarayya na NNPP a Kano

A wani labarin, Legit Hausa ta rahoto a baya cewa kotun sauraron kararrakin zaben 'yan majalisun tarayya ta tsige Idris Dankawu na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) daga kujerar dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Kumbotso ta jihar Kano.

Channels Tv ta rahoto cewa kotun ta tsige Dankawu kan kirkirar takardar jarrabawarsa ta WAEC wacce ya gabatar domin shiga zaben da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng