Ministan Ayyuka Ya Yi Wa ‘Dan Kwangila Kaca-Kaca a Fili Kan Mummunan Aikin Titi

Ministan Ayyuka Ya Yi Wa ‘Dan Kwangila Kaca-Kaca a Fili Kan Mummunan Aikin Titi

  • David Umahi bai ji dadin aikin da ya gani a titin Amanwozuzu-Uzoagba-Eziama-Orie-Amakohia ba
  • Ministan ayyukan na Najeriya ya soki kamfanin Fig Fyne Construction Company da aka ba kwangilar
  • Sanata Umahi ya nuna ba zai biya sisin kobo ba, ya ce kyau ‘dan kwangilar ya ji kunyan abin da ya yi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Imo Ministan ayyuka, David Umahi ya nuna takaicinsa a game da aikin titin Amanwozuzu-Uzoagba-Eziama-Orie-Amakohia a jihar Imo.

A wani bidiyo Legit Hausa ta ci karo da shi a shafukan Tik Tok da X, an ji Sanata David Umahi ya na Allah-wadai da wani ‘dan kwangila.

Gwamnatin tarayya ta na kokarin gyara babban titin Amanwozuzu-Uzoagba-Eziama-Orie-Amakohia da ke karamar hukumar Ikeduru a Imo.

UMahi
Ministan ayyuka, David Umahi Hoto: @isaajibola
Asali: Twitter

A gaban jama’a aka ji ministan ya na sukar aikin kamfanin Fig Fyne Construction Company, ya yi barazanar karbe kwangilar da aka ba su.

Kara karanta wannan

Mu ba Sakarkaru ba ne: Abin da Ya sa Wike Ya Dage Sai Ya Karya PDP - Mutumin Atiku

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dave Umahi ya ba Fig Fyne Construction Company shawarar su hada-kai da wani kamfani da ya san aiki domin a samu a kammala ginin titin.

Tsohon gwamnan ya ce dole ayi aikin da kyau saboda a sharewa mutanen yankin hawaye, musamman ganin daga nan ’dan kwangilar ya fito.

"Ka ji kunya"- Umahi

Saboda haka Umahi yake cewa ya kamata 'dan kwangilar ya ji kunyar aikinsa.

Kamfanin ya ce ya yi aikin kilomita biyar, amma a bidiyon da Fasto Okezie J. Atani ya wallafa, ministan ya ce bai ga alamar an yi titi a wurin ba.

Duk da haka, ministan kasar ya jinjinawa kamfanin a kan yadda su ka sake tsara aikin – an kara fadin titin, sannan an yi hanyar wucewar ruwa.

Gwamnatin Tinubu ba za ta biya kudin aiki ba

Kara karanta wannan

Nyesom Wike: Kwanaki da Shiga Ofis, Minista Ya Bada Ayyukan Tituna 135 a Abuja

Ministan ya ce kamfanin su rubuta takarda a tsaida biyan wasu kudin kwangila wanda ya zarce N1bn, sai sun amince za su yi abin da ya dace.

Takardu sun nuna gwamnatin tarayya ta biya N495m, amma ministan ya ce ba zai karasa biyan ragowar N840m muddin ba ayi aiki mai nagarta ba.

Mutanen kudu maso gabas su na shan wahalar karanci da rashin kyawun tituna, Umahi ya ce dole a tausaya masu, ya na mai tir da aikin da ya gani.

Amsar da 'Dan kwangila ya bada

‘Dan kwangilar ya ce manyan motoci ne su ke lalata masu aiki kuma ya nuna tun farko ba ayi hanyar ta yadda motoci masu nauyi za su rika bi ba.

Kamfanin ya nuna ba zai yi rigima da ministan ba, amma ya yi kokarin ankarar da shi cewa gwamnatin Najeriya ba ta biya su kudin kwangilar ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng