Gwamnatin Tinubu Ta Shiga Binciken CBN da NIRSAL, Cikin Ma’aikata Ya Ɗuri Ruwa

Gwamnatin Tinubu Ta Shiga Binciken CBN da NIRSAL, Cikin Ma’aikata Ya Ɗuri Ruwa

  • Jami’in da Bola Tinubu ya dauko domin ya yi bincike na musamman a kan CBN ya soma yin aiki
  • Shugaban ‘yan sanda ya ba Jim Obazee aron DCP Eloho Edwin Okpoziakpo domin taya shi bincike
  • Ma’aikatan da ke hukumar NIRSAL su na cikin fargaba, za a iya tono badakalar da aka yi a baya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Ma’aikata sun rude a babban bankin CBN da hukumar NIRSAL, inda aka shiga bincike na musamman a kan abubuwan da su ka faru a baya.

Bayanan Daily Trust ya nuna mai binciken musamman da Bola Tinubu ya kafa domin bankado gaskiyar barnar da aka tafka a CBN ya soma aiki.

Kwanaki bayan dakatar da Mista Godwin Emiefele, sai aka ji Mai girma Bola Tinubu ya ba Mista Jim Obazee nauyin yin bincike a kan babban bankin.

Kara karanta wannan

Gwamnan CBN, EFCC, Hafsun Soji da Mutanen Buhari da Tinubu Ya Kora a Kwana 100

Tinubu
Bola Tinubu a kasar waje Hoto: @Dolusegun
Asali: Twitter

IGP ya karfafa gwiwar Jim Obazee

Saboda ya ji dadin yin aiki, Obazee ya aika takarda zuwa ga Sufetan ‘Yan sanda a watan Agusta, ya nemi a ba shi jami’an da za su taimaka masa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoton ya ce ranar 6 ga Satumba, IGP ya maidawa jami’in amsa a wata takarda ta hannun CP Abaniwonda S. Olufemi, ya amince da bukatarsa.

Wadanda za su binciki CBN

Jami’an ‘Yan sandan da aka Obazee a matsayin wadanda za su taya shi aikin na sa su ne: DCP Eloho Edwin Okpoziakpo; da kuma CSP Celestine Odo.

Jaridar ta ce rgowar jami’an tsaron da za su gudanar da bincike a kan CBN da hukumar NIRSAL CSP Segun Aderoju da kuma DSP Tijani A. Bako.

Kudin da su ka yi kafa za su dawo

Tinubu ya bada umarnin a karbo duk kudin da aka ware da sunan tsarin noma. Legit ta na da labari an fara karbo bashin kudin da ke hannun mutane.

Kara karanta wannan

Tsere-Tsere Yayin Da CBN Ya Kama Dan Canji Kan Siyar Da Dala Kasa Da 700 , Ya Bayyana Yadda Ya Kamata A Siyar

Majiya ta ce wasu daidaiku da ake zargi su na da hannu a badakalar aikin noma sun tsure da binciken ya shafi aikin noman alkalama a Kano da Jigawa.

Ana zargin akwai hadimin tsohon gwamnan CBN da ke da asusu fiye da 44 a bankuna da wani jami’i da ake kashe N600, 000 a kula da karnukansa.

Rahoton ya kara da cewa IGP ya dauko Edwin Okpoziokpo ya taimakawa binciken ne domin ya yi aiki da shi a lokacin da ya ke rike da sashen FCIID a Abuja.

Ana yi wa DCP Eloho kallon jami’i mai gaskiya da son gyara. A bangaren karatun boko, ya na da ilmin shari’a kuma ya kware a binciken satar yanar gizo.

Da jin labarin binciken, wasu ma’aikatan NIRSAL sun fara tarwatsa takardun da za a iya kafa hujja da su, zargin da wani jami’i na hukumar ya karyata.

An yi barna a bankin CBN

Kara karanta wannan

Hukuncin Kotu: Rabaran Mbaka Ya Gaya Wa Shugaba Tinubu Ya Shirya Barin Ofis? Gaskiya Ta Bayyana

Kwanaki da ram da Godwin Emefiele, sai aka ji labari DSS ta kama Shugaban NIRSAL, kwanaki kuma aka tsare wata mataimakiyar gwamnan CBN.

Tsohon Gwamnan CBN bai rasa danganta da Abbas Umar Masanawa da su ka yi aiki tare a lokacin da Umar Dangiwa yake cewa an yi rashin gaskiya iri-iri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng