Wata Mata Ta Faɗi Ta Mutu a Gabas Mile 2 Da Ke Jihar Legas

Wata Mata Ta Faɗi Ta Mutu a Gabas Mile 2 Da Ke Jihar Legas

  • Mutane sun shiga yanayin tashin hankali da baƙin ciki a gadar Mile 2 yayin da wata mata ta faɗi kuma rai ya yi halinsa nan take yau da safe
  • Shaidun gani da ido sun bayyana cewa matar, wacce har yanzu ba a gano bayananta ba, tana cikin tafiya a gadar, ba zato ta faɗi
  • Mahukunta sun fara gudanar da bincike domin gano sunanta da sauran bayanan mamaciyar, da kuma iyalanta

Jihar Lagos - Da sanyin safiyar yau Litinin, wani lamari mai ban tsoro ya faru a gadar Mile 2 da ke jihar Legas, yayin da wata mata da har yanzu ba a tantance ba ta fadi ta mutu.

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa waɗanda lamarin ya auku a kan idonsu sun bayyana cewa matar tana cikin tafiya a kan gadar, ba zato ba tsammani ta yanke jiki ta faɗi.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Rayukan Mutane Da Dama Sun Salwanta a Wani Hatsarin Jirgin Ruwa a Arewacin Najeriya

Wata mata ta kwanta dama a Gadar Mile 2.
Wata Mata Ta Faɗi Ta Mutu a Gabas Mile 2 Da Ke Jihar Legas Hoto: vanguardngr
Asali: UGC

Wani ɗan Okada, wanda ya faɗa wa 'yan jarida iya abinda ya gani, ya ce:

"Tana ƙoƙarin hawa kan Mashin kawai ba zato sai ta faɗi, da fari na yi tunanin haka nan ta faɗi amma daga bisani alamu suka tabbatar da akwai matsala lokacin da ta daina numfashi."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Lamarin dai ya janyo ɗimbin jama’a da suka yi dafifi suna kallon al’amarin da ya auku mai ban tsoro, inda suka yi matuƙar baƙin ciki da wannan abin takaici.

Har kawo yanzu ba a tantance wacece matar ba kuma daga ina fito da kuma babban maƙasudin abinda ya yi ajalinta a lokaci guda.

Wane mataki mahukunta suka ɗauka a yanzu?

A halin yanzu, rahotanni sun nuna cewa mahukuntan wurin sun fara kokarin gano bayanan matar, iyalanta kana su gudanar da bincike kan yanayin da ya jawo mutuwarta.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Hatsarin Jirgin Ya Laƙume Rayukan Mutane Sama da 10 a Jihar Arewa

Har yanzun rundunar 'yan sanda reshen jihar Legas ko ɓangaren gwamnati ba su fitar da sanarwa a hukumance kan lamarin ba, rahoton Jaridar News Beat ya tattaro.

Mutane 15 Sun Mutu Yayin da Jirgin Ruwa Ya Nutse a Jihar Adamawa

A wani rahoton na daban Jirgin ruwa ya nutse da mutane sama da 20, ana fargabar mutum 15 daga cikin sun kwanta dama a jihar Adamawa.

Wani ganau ya ce lamarin ya faru ne yayin da wata iska mai ƙarfi ta riƙa tunkuɗo ruwa yana shiga cikin jirgin da yammacin ranar Jumu'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262