‘Yan Bindiga Sun Yi Ta’adi, Sun Sace Mai Daki da Yarinyar ‘Dan Sanda Har Gida
- ‘Yan bindiga sun shiga gidan wani jami’in ‘dan sanda a Jalingo, har su ka harbe shi da bindiga
- Miyagun sun yi garkuwa da mata da diyar ‘dan sandan, jami’an tsaro su na sa ran a kubutar da su
- Wata mata da aka bindige a gidan ta sheka barzahu kamar yadda likitoci su ka tabbatar a asibiti
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Taraba - Wasu miyagu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kashe wata mata a safiyar Lahadin da ta gabata a birnin Jalingo da ke jihar Taraba.
Rahoto da aka samu a Premium Times ya tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a unguwar Mile 6.
Baya ga kisan da su ka yi, ‘yan bindigan sun yi awon gaba da mata da kuma diyar wani jami’in ‘dan sanda, har yanzu ba a san inda su ke ba.
Garkuwa da mutane a Taraba
Wannan na cikin labaran da aka samu na garkuwa da mutane da-dama da aka yi a cikin makonni biyu a babban birnin na Arewa maso gabas.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kafin yanzu, an ji yadda ‘yan bindiga su ka yi garkuwa da mutane fiye da 10 a Mayo Dassa duk a garin na Jalingo, amma an samu sun tsira.
Kakakin ‘yan sandan jihar Taraba, Usman Abdullahi ya tabbatarwa manema labarai aukuwar wannan labari mara dadi cikin karshen mako.
Yadda abin ya faru - 'Yan Sanda
Usman Abdullahi ya ce an harbi wani ‘dan sanda da ke aiki da rundunar jihar Ribas kuma an dauke mai dakinsa da diyarsa.
Sannan an harbe wata mata wanda daga baya aka tabbatar da ta mutu da aka je asibiti.
"Masu garkuwa da mutanen sun haura katanga ne su ka dauke wani jami’i da ke aiki da ‘yan sandan Ribas mai suna Gamaliel.
Jami'an 'Yan Sanda A Kano Sun Dauki Mummunan Mataki A Kan Masu Hawa Ba Bisa Ka'ida Ba, Bayanai Sun Fito
A yunkurin haka su ka yi garkuwa da diyarsa da matarsa. Su ka harbe shi tare da wata mata a gida.
Da aka je babbar cibiyar lafiya ta tarayya a Jalingo aka tabbatar da matar ta mutu. Ana kokarin ceto su ba tare da kwarzane ba."
- Usman Abdullahi
Majiya ta shaida masu garkuwa da mutanen sun zo ne da makamai, su ka tafi gidan wani limamin coci, da ba su same shi, su ka tafi gidan ‘dan sanda.
James Ngilari a kurkuku
Idan aka dauki shari’ar da aka yi da James Bala Ngilari, an rahoto tsohon gwamnan ya ce babu daya da aka yi maganar karkatar da dukiyar jama’a.
Tsohon Gwamnan Adamawan da ya je gidan yari zai suma idan ya yi ido-biyu da Naira Biliyan 1, ya ce gaskiyarsa ta hana shi zama Sanata a APC.
Asali: Legit.ng