Kotun Ta Alanta Bayyana Dan Takarar PDP Suswam a Matsayin Wanda Ya Lashe Zaben Kujerar Sanatan Benue

Kotun Ta Alanta Bayyana Dan Takarar PDP Suswam a Matsayin Wanda Ya Lashe Zaben Kujerar Sanatan Benue

  • Sanata Suswan ya yi nasara a kan zababben sanatan APC a zaben da aka gudanar a Najeriya a ranar 25 ga watan Faburairu
  • Kotun daukaka kara ta kori sanata Emmanuel bisa gamsuwa da hujjojin da aka gabatar a gabanta a zaman sauraran kara
  • An kori wani dan majalisar da ya yi takara a karkashin jam'iyyar NNPP a jihar Kano, lamarin da ya dauki hankali sosai

Jihar Benue - Kotun sauraren kararrakin zaben Majalisar Tarayya da ke zamanta a Makurdi, babban birnin Jihar Benue, ta kori Emmanuel Udende na Jam’iyyar APC tare da bayyana Gabriel Suswam na Jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben Sanatan Benue.

Shugaban kwamitin alkalan, Zik-Ikeorha da wani mamba sun bayyana hukuncin da ya yiwa tsohon Gwamnan cewa Suswam da PDP dadi, AIT ta tattaro.

Kara karanta wannan

Ahaf: Rashin Gaskiya Ta Sa Kotu Ta Tsige Dan Majalisar NNPP a Kano, An Ba Dan Takarar APC

Hukuncin ya nuna cewa, PDP da Suswam sun cika sharuddan da doka ta tanada wajen tabbatar da hujjarsu ta bayyana rashin bin doka da oda, rashin sanya hannu kan takardun zabe da kuma kwange a zaben da ya gabata.

An kori Emmanuel Udende daga kujerar sanata
Yadda aka kori Emmanuel Udende daga kujerar sanata | Hoto: Emmanuel Udende, Gabriel Suswam
Asali: Facebook

Yadda abin ya faro tun farko

An ayyana Sanata Udende a matsayin wanda ya lashe zaben sanata da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023 bayan ya samu kuri'u 135,573 inda ya doke Sanata Gabriel Suswam na jam'iyyar PDP wanda ya samu kuri'u 112,231, Vanguard.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanata Suswam bai gamsu da sakamakon zaben ba, inda ya tunkari kotun da cewa zaben na dauke da aringizon kuri’u, rashin bin ka’ida, sauye-sauye da kuma gurbata sakamako.

Tsohon Gwamnan ya kalubalanci sakamakon zaben ne daga rumfunan 474 a fadin kananan hukumomi biyar da gundumomi a shiyyar Sanatan mai kunshe da kananan hukumomi bakwai masu rumfunan zabe 1,844.

Kara karanta wannan

Ta leko ta koma: Kotu ta tsige fitaccen dan majalisar wakilai na PDP, ta fadi dalili

An tsige dan majalisar NNPP a Kano

A wani labarin, kotun sauraren kararrakin zabe ta Kano ta soke zaben dan majalisar wakilai mai wakiltar Kura/Madobi/Garun Malam a majalisar wakilai.

Kotun dai ta danganta tsige dan majalisar wakilan na jam’iyyar NNPP ne bisa gaza yin murabus daga aikinsa a jami’ar Bayero ta Kano kwanaki 30 gabanin zaben, Daily Trust ta ruwaito.

Don haka mai shari’a Ngozi Azinge ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da ta ajiye takardar shaidar cin zabe da aka baiwa Datti a baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.