Yadda Aka Bankado Wasu Gwangwanayen Timatir da Aka Boye Miyagun Kwayoyi a Ciki

Yadda Aka Bankado Wasu Gwangwanayen Timatir da Aka Boye Miyagun Kwayoyi a Ciki

  • Jami'an hukumar NDLEA sun kama wasu kayayyakin timatir da ake fargabar miyagun kwayoyi ne a ciki
  • An ce an makare gwangwanayen timatir din ne da miyagun kwayoyi don gujewa bincike da kamun NDLEA
  • Ana yawan kame wadanda ke shigo da miyagun kwayoyi da kayan maye a yankuna daban-daban na Najeriya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Najeriya - Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta gano wasu miyagun kwayoyi da aka boye a cikin gwangwanayen timatir.

Daraktan yada labarai na NDLEA, Femi Babafemi ne ya bayyana haka a wani sako da ya wallafa a Facebook a ranar Lahadi, 10 ga watan Satumba.

Yadda aka yi basajar kwaya a gwangwanin timatir
Gwangwanayen timatir da aka saka kwaya | Hoto: NDLEA
Asali: Facebook

Bayanai kan yadda aka gano miyagun kwayoyin

Da yake yada bidiyo da hotunan kayayyakin da aka kwato, Babafemi ya rubuta:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

“Aikin Mijinta Ne”: Hotunan Yadda Ayarin Motocin Matar Gwamnan Bauchi Suka Makale a Tabo

“Wannan wani dalili ne da ya sa muke gaya muku cewa hankulan wasu mutane na da hadari kamar yadda wannan hoton bidiyon ya nuna lokacin da jami’an NDLEA suka bankado gwangwanayen timatir da aka yi amfani da su wajen boye miyagun kwayoyi.
"Ku haskaka idanunku, ku kula da abin da kuke karba daga hannun jama'a."

Kalli bidiyon:

An kama masu kawo kwayoyi Najeriya daga waje

A bangare guda, an kama wasu mutanen da ke safarar miyagun kwayoyi da suka shigo Najeriya daga Qatar.

Rahoton ya bayyana cewa, an kama su ne a filin jirgin saman Murtala Muhammad da ke birnin Legas a Kudu maso Yammacin Najeriya.

Ya zuwa lokacin, an ce ana ci gaba da bincike don gano irin barnar da suke aikatawa da kuma abin da suka aikata a yanzu.

An kama jami'an NDLEA da kwaya

Jami'an 'yan sanda a jihar Legas sun cafke wani da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi wanda ya yi ikirarin cewa shi jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ne a ranar Lahadi, 12 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Gwamnan PDP Ya Saka Tukwicin N100m Kan Makashin DPO, Ya Dakatar Da Basarake Har Sai Baba Ta Gani

A lokacin da aka cafke wanda ake zargin, an same shi dauke da ƙwayar 'Marsh-Mallow' mai nauyin kilogiram 4, rahoton Daily Trust ya tabbatar.

Wanda ake zargin mai suna Kelechi Chukwumeeije, ya shiga hannun jami'an 'yan sanda ne a karkashin jagorancin ASP Samuel Sunday.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.