Gwamnan Arewa Zai Fara Kama Yaran Da Aka Gani a Titi a Lokacin Makaranta

Gwamnan Arewa Zai Fara Kama Yaran Da Aka Gani a Titi a Lokacin Makaranta

  • Gwamnatin jihar Taraba za ta fara kama iyayen da yaransu ke yawo a titi a lokacin makaranta
  • Kwamishinar ilimi ta jihar Taraba, Dr Augustina Godwin, ta ce za a ci tarar duk iyayen da aka kama yaransu basa zuwa makaranta
  • Gwamnan Taraba, Agbu Kefas, dai ya mayar da ilimin firamare da na sakandare kyauta a jiharsa

Jihar Taraba - Kwamishinar ilimi ta jihar Taraba, Dr Augustina Godwin, ta ce gwamnatin jihar ta kafa wani kwamiti domin kama duk yaron da ya kamata ace yana makaranta a titi a lokacin makaranta.

Agustina ta ce za a gano inda iyayen yaron suke don yiwuwar kama su da hukunta su, jaridar Leadership ta rahoto.

Gwamnan Taraba zai dunga kama yaran da basa zuwa makaranta
Gwamnan Arewa Zai Fara Kama Yaran Da Aka Gani a Titi a Lokacin Makaranta Hoto: Agbu Kefas
Asali: Facebook

Kwamishinar ta bayyana hakan ne a ranar Asabar, 9 ga watan Satumba, a Jalingo, babban birnin jihar Taraba yayin da take amsa tambayoyi daga manema labarai.

Kara karanta wannan

Kaico: Kawaye sun lakadawa wata mata duka kan wawashe kudi a wurin biki

Ta kuma ce Gwamna Agbu Kefas ya mayar da ilimi kyauta kuma wajibi ga duk yaran da suka isa makaranta ba tare da la’akari da kabila, addini, siyasa ko matsayi ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Har wayau, ta ce gwamnan ya ware kudi don tafiyar da harkokin dukkan makarantun gwamnati domin aiwatar da tsarin ilimi kyauta.

Sannan ta ce gwamnan bai shirya karbar kowani uzuri daga iyaye ba idan aka kama yaron da ya kamata ace yana makaranta yana yawo a titi a lokacin makaranta.

Za a ci tarar duk iyayen da aka kama

Ta yi kira ga iyayen da ke da yara fiye da daya da kada su yi kasa a gwiwa wajen kai dukka yaran makarantu, tana mai cewa manufar ilimin bai kayyade adadin yaran da ya kamata iyaye su saka a makarantu ba.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Gwamnan PDP Ya Saka Tukwicin N100m Kan Makashin DPO, Ya Dakatar Da Basarake Har Sai Baba Ta Gani

"Za mu kama duk yaran da ya kamata ace yana makaranta amma aka gan sa yana yawo a titi a jihar a lokacin makaranta. Za mu gano inda iyayensu suke sannan mu kama su don yiwuwar hukunta su; mun kafa doka a kan haka. Akwai tara da irin wadannan iyaye za su biya na kin bin doka.
“Gwamnan ya bayyana cewa an riga an biya kudin kayan koyarwa kuma za a fara rabon kayan daga mako mai zuwa da zaran an koma makarantu. Gwamnan ya kuma bayyana cewa za a fara rabon kayan makaranta a watan Janairun 2024.
"Tsoffin dalibai daga makarantun Firamare da sakandare su ci gaba da aiki da tsoffin inifam dinsu yayin da sabbin shiga za su ci gaba da amfani da kayan da suka zo da shi har zuwa lokacin da kayan makarantar za su iso a shekara mai zuwa," cewarta.

Kwamishinar ta kuma bayyana cewa ma'aikatar za ta sauya tsarin sa idonta domin kula da yadda malamai da dalibai ke bin manufar da kuma gano kalubalen da ba a hango zuwansu ba.

Kara karanta wannan

Hukuncin Kotun Zabe: A Karshe Peter Obi Ya Aika Gagarumin Sako Ga Mabiyansa

Gwamnonin Arewa Maso Gabas Sun Bukaci Dakarun Sojoji Su Kakkabe 'Yan Ta'adda

A wani labarin, mun ji cewa kungiyar gwamnonin jihohin Arewa maso Gabashin Najeriya, sun buƙaci dakarun sojoji da su farmaki maɓoyar ƴan ta'addan da suka ƙi miƙa wuya su halaka su.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa gwamnan jihar Borno kuma shugaban ƙungiyar, Farfesa Babagana Umara Zulum, shi ne ya yi wannan kiran a wajen taron ƙungiyar karo na takwas, ranar Asabar, 9 ga watan Satumba a birnin Maiduguri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng