Rashin Tsaro: Sarkin Birnin Gwari Ya Musanya Hakimai Biyu
- Sarkin Birnin Gwari, Mai martaba Malam Zubairu Jibril, Maigwari II ya sauyawa wasu hakimai biyu a masarautarsa fada saboda yanayin tsaro
- An dauki Alhaji Yusuf Yahaya Abubakar, Sarkin Kudun Birnin Gwari zuwa yankin Kuyello
- Masarautar ta dauke Alhaji Alhassan Alhassan, Ubandawakin Jarumawan Birnin Gwari daga yankin Kuyello zuwa yankin Birnin Gwari ta tsakiya
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kaduna - Daga cikin kokarin da yake yi na inganta lamarin tsaro a masarautarsa, Sarkin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna, Malam Zubairu Jibril, Maigwari II ya amince da musanya wasu hakimai biyu a masarautarsa.
An yi wa Sarkin Kudun Birnin Gwari da Ubandawakin Jarumawan Birnin Gwari musanyar fada
Wata sanarwa daga sakataren majalisar masarautar, Mukhtar Salisu Muhammad, ta ce an mayar da Alhaji Yusuf Yahaya Abubakar (Sarkin Kudun Birnin Gwari) zuwa yankin Kuyello.
Fitaccen Sarkin Arewa Ya Tara Sarakuna, Ya Yi Barazanar Tsige Duk Wanda Ya Haɗa Baki da 'Yan Bindiga
Sannan an dauke Alhaji Alhassan Alhassan (Ubandawakin Jarumawan Birnin Gwari) daga yankin Kuyello zuwa yankin Birnin Gwari ta tsakiya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sanarwar ta yi umurnin cewa a kammala mikawa da kuma karbar ragamar mulkin cikin gaggawa, rahoton Nigerian Tribune.
A halin da ake ciki, sabon hakimin Birnin Gwari ta tsakiya Alhaji Alhassan Alhassan (Ubandawakin Jarumawan Birnin Gwari) ya dade da kama aiki.
Alhassan wanda ya samu rakiyar yan uwa, abokai da masu fatan alkhairi zuwa sabuwar fadarsa, ya yi alkawarin aiki tukuru don ci gaban masarautar.
Ya ce zai marawa duk matakin da sarkin zai dauka baya don kawo karshen matsalar tsaro da masarautar ke fuska.
Yan bindiga sun sace mutane 7 tare da halaka manomi a jihar Kaduna
A wani labarin, mun ji cewa yan ta'adda da ake zaton masu garkuwa da mutane ne, sun halaka mutum ɗaya tare sace wasu mutane bakwai a Unguwar Gajere da ke mazaɓar Kutemeshi da ke ƙaramar hukumar Birnin Gwarin jihar Kaduna.
An bayyana cewa lamarin dai ya faru ne ranar Laraba, 2 ga watan Agustan shekarar 2023, inda maharan suka farmaki mutanen yayin da suke aiki a gonakinsu.
Dan Majalisar jihar da ke wakiltar mazaɓar Kakanga ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce 'yan bindigan sun kuma yi awon gaba da dabbobi masu tarin yawa a wasu ƙauyuka da ke makwabtaka da su.
Asali: Legit.ng