Wani Mutum Ya Wulakanta Alqur'ani Mai Tsarki A Gaban Ofishin Jakadancin Turkiyya Da Ke New York

Wani Mutum Ya Wulakanta Alqur'ani Mai Tsarki A Gaban Ofishin Jakadancin Turkiyya Da Ke New York

  • Abin takaici yayin da aka sake samun wani mutum ya ci zarafin Alqur'ani mai tsarki a birnin New York da ke Amurka
  • A cikin wani faifan bidiyo da ake yadawa an gano mutumin na jifa tare da tattaka Alqur'ani a gaban ofishin jakadancin Turkiyya da ke New York
  • Wannan na zuwa ne mako daya bayan magajin birnin New York ya bai wa Musulmai damar jiyar da kiran sallah ba tare da neman izini ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

New York, Amurka - Wani mutum a birnin New York na Amurka ya ci mutuncin Alqur'ani a bainar jama'a.

Mutumin ya jefar da Alkur'ani mai tsarki a kasa tare da tattaka shi a bakin ofishin jakadancin Turkiyya da ke New York.

Wani ya wulakanta Alqur'ani a birnin New York
Jami'an Tsaro Sun Kori Mutumin Da Ya Wulakanta Alqur'ani A New York. Hoto: TRT World.
Asali: Facebook

An ci zarafin Alqur'ani a New York

Kamfanin dillancin labaran Anadolu na kasar Turkiyya ya rawaito cewa lamarin ya faru ne ranar Juma'a 8 ga watan Satumba da misalin karfe 2:46 na yamma.

Kara karanta wannan

Jami'an 'Yan Sanda A Kano Sun Dauki Mummunan Mataki A Kan Masu Hawa Ba Bisa Ka'ida Ba, Bayanai Sun Fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami'an tsaro a ofishin jakadancin kasar Turkiyya sun dauki mataki inda suka yi gaggawar fitar da mutumin daga wurin.

Rahotanni sun tabbatar cewa Alkur'ani mai tsarkin da mutumin ya wulakanta an fassara shi da harshen Ingilishi ne.

Matakin jami'an tsaro kan cin zarafin Alqur'ani

An shaida wa Jami'ai a ofishin rundunar 'yan sandan New York (NYPD) da Jami'an Tsaron Farin Kaya (DSS) a ofishin Jakadanci faruwar lamarin, TRT World ta tattaro.

A cikin wani faifan bidiyo da ake yadawa a kafafen sadarwa an jiyo mutumin na cewa "wannan Alqur'ani ne" yayin da ya ke jifa tare da tattaka shi.

Wannan na zuwa ne bayan magajin birnin New York a makon da ya gabata ya bai wa Musulmai damar jiyar da kiran sallah a ranakun Juma'a da kuma watan Ramadan.

Legit.ng Hausa ta ji ta bakin wasu kan wannan matsalar.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Sake Kai Mummunan Hari Wurin Ibada a Jihar Kaduna, Sun Kashe Malami

Muhammad Yusuf ya ce wannan abin takaici ne ganin yadda Musulmai ke mutunta ko wane littafi.

Ya ce:

"Gaskiya abin bakin ciki ne ganin yadda littafi ne da ya fi ko wane daraja.
"Karin abin haushi ma shi ne yadda Musulmai ba sa wulakanta Bible ko ma littafin addinin Hindu.
"Mafi yawancin masu irin haka ba sa mutunta addininsu ma shiyasa su ke aikata haka."

Usman Farouk tambaya ya yi da cewa shin wane riba su ke samu da yin haka? ya ce abin da zai fada kawai shi ne Allah ya shirye su.

Yayin da Ustaz Muhammad Adamu ya ce matsala ce wacce ta tsolewa wadanda ba Musulmai ba ido.

Hakan ba zai hana Musulunci ci gaba da yaduwa ba a duniya, inda ya ce alama ce ta bunkasar addinin a duniya tun da ai mai hujja ba ya fada.

Sultan ya yi Allah wadai da kona Alqur'ani a Sweden

Kara karanta wannan

Giro Argungu: Atiku Abubakar Ya Mika Sakon Ta'aziyyarsa Ga Iyalan Malamin

A wani labarin, Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar ya yi Allah wadai da cin zarafin Alqur'ani mai tsarki da wani dan Iraqi ya yi a kasar Sweden.

Sultan ya ce wannan aika-aika wulakanci ne da kuma neman tsokana zuwa ga addinin Musulunci duk kasashe na ikirarin kare hakkin addinai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.