Gwamnatin Abba Gida Gida Ta Amince Da Biliyan 4.8 Don Gudanar Da Ayyuka Daban-Daban

Gwamnatin Abba Gida Gida Ta Amince Da Biliyan 4.8 Don Gudanar Da Ayyuka Daban-Daban

  • Majalisar zartarwa ta jihar Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta amince da sakin naira biliyan 4.8 don aiwatar da ayyuka daban-daban a jihar
  • Abba gida gida ya ce daga cikin kudin za a yi amfani da N79,284,538 wajen fara aikin gyara makarantun sakandare
  • Ya ce za'a yi aikin gyara makarantun kwana 11 da gwamnatin baya ta wofantar tare da kulle su

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta ce ta amince da sakin kudi naira biliyan 4.8 domin aiwatar da ayyuka daban-daban a jihar.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X da aka fi sani da Twitter a ranar Asabar, 9 ga watan Satumba.

Abba Kabir Yusuf ya amince da sakin kudade don aiwatar da ayyuka daban-daban
Gwamnatin Abba Gida Gida Ta Amince Da Biliyan 4.8 Don Gudanar Da Ayyuka Daban-Daban Hoo: @Kyusufabba
Asali: Twitter

Gwamnatin Abba gida gida za ta gyara makarantun kwana 11 da aka rufe

Kara karanta wannan

Tinubu: Gwamnan PDP Ya Manna Hotonsa a Jikin Buhunan Shinkafa, Ya Faɗi Dalili

Ya ce majalisar zartarwa ta jihar yayin zamanta na ranar Alhamis da ta gabata, ta amince da sakin kudi kimanin N79,284,538 domin fara aikin gyaran makarantun sakandare na kwana guda 11.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar Abba Gida Gida, wadannan makarantu sune wadanda gwamnatin Abdullahi Ganduje ta wofantar tare da kullesu.

Sanarwar ta ce:

"A yayin zaman majalisar zartarwa karo na biyar (5th) wanda ya gudana ƙarƙashin kulawa ta ranar alhamis da ta gabata na amince da sakin kuɗi kimanin Naira miliyan 79 da dubu 284 da ɗari 538 domin a fara aikin gyaran makarantun sakandare na kwana guda 11 waƴanda gwamnatin da ta gabata ta wofantar tare da kulle su.
"Wannan kuɗi na daga cikin wani ɓangare na kuɗaɗe kimanin Naira biliyan 4 da miliyan 882 da dubu 378 da naira 71 da na saki domin gudanar da wasu ayyuka daban-daban a wannan jaha namu mai albarka."

Kara karanta wannan

Mai Neman Karbe Kujerar NNPP Ya Kunyata, Alkali Ya Ce a Biya ‘Dan Majalisa N100, 000

An cigaba da biyan mahaifinsu albashi da ya rasu, matashi ya maidawa gwamna kudin

A wani labari na daban, mun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya jinjinawa wani matashi, Yusuf Sulaiman Sumaila wanda ya nuna gaskiya da bin doka.

Wannan Bawan Allah ya dauki albashin da aka biya mahaifinsu da ya rasu, sai ya maida cikin baitul-malin jihar Kano domin ba hakkinsa ba ne.

Mai taimakawa Gwamnan Kano a dandalin sada zumunta na zamani, Abdullahi Ibrahim ya bayyana haka a shafin X da aka fi sani da Twitter.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng