Gwamna Yahaya Bello Ya Sha Alwashin Dawo Da Kujerun Sanatocin Da Kotu Ta Karba a Hannun APC a Kogi
- Gwamnan Yahaya Bello ya sha alwashin dawo da kujerun sanatocin da jam'iyyar APC ta rasa a jihar Kogi
- Jam'iyyar APC ta rasa kujerun sanatoci biyu a kotun zaɓe hannun ƴan takarar jam'iyyar PDP a kotun zaɓe
- Gwamnan ya sha alwashin cewa duka kujerun sanatoci biyun da APc ta rasa, za ta dawo da su a kotun ƙoli
Jihar Kogi - Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya sha alwashin cewa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) za ta ƙwato kujerun sanatoci biyu da ta rasa a kotun zaɓe a hannun jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
Gwamnan ya sha wannan alwashin ne baya kotun zaɓe ta kwace kujerun sanatocin Kogi ta Gabas da Kogi ta Tsakiya, cewar rahoton PM News.
Wane kujerun sanatoci APC ta rasa a Kogi?
Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ta soke zaɓen Sanata Jibrin Isah Echocho, sanatan Kogi ta Gabas bisa dalilin cewa an soke zaɓe a rumfunan zaɓe 94.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ƙarar wacce ɗan takarar PDP, Victor Udeji ya shigar, kotun ta kuma ba hukumar zaɓe ta INEC umarnin sake zaɓe a rumfunan zaɓen guda 94 da aka soke zaɓensu.
Haka kuma kotun zaɓen ta soke nasarar Abubakar Ohere na jam'iyyar APC, a zaɓen sanatan Kogi ta Tsakiya sannan ta bayyana Natasha Akpoti ta jam'iyyar PDP a matsayin wacce ta lashe zaɓen.
Kotun ta bayyana cewa an yi wa Ohere aringizon ƙuri'u a rumfunan zaɓe tara na ƙaramar hukumar Ajaokuta.
Kotun ta ce hujjojin da aka gabatar a gabanta sun nuna cewa an rage yawan ƙuri'un da Natasha ta samu.
Gwamna Bello ya sha alwashi
Hukuncin Kotu: An Bayyana Wani Muhimmin Dalili Da Zai Sanya Shugaba Tinubu Ya Cigaba Da Nasara Akan Atiku Da Peter Obi
Sai dai, gwamna Yahaya Bello a ranar Alhamis ya gayawa manema labarai a fadar shugaban ƙasa cewa APC za ta dawo da kujerun biyu daga hannun ƴan takarar PDP a kotun ƙoli, rahoton Channels tv ya tabbatar.
Ya ƙara da cewa a ƙarshe APC ce za ta kasance da kujerun sanatoci uku da ta lashe zaɓensu a zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairu.
"Ina son na ba ku tabbacin cewa, duba da hukuncin da aka yanke a kotun ɗaukaka ƙara, za mu samu sanatoci uku bisa uku a jihar Kogi, ina baku tabbaci." A cewarsa.
Kotu ta tabbatar da nasarar sanatan APC a jihar Oyo
A wani labarin na daban, kotun sauraron ƙararrakin zaɓen jihar Oyo ta tabbatar da nasarar sanatan Oyo ta Kudu, Sharafadeen Abiodun Alli na jam'iyyar APC.
Kotun ta yi watsi da ƙarar da dan takarar sanata na jam'iyyar PDP, Joseph Tegbe ya shigar yana mai ƙalubalantar nasarar lashe zaɓen da Sanata Sharafadeen ya yi.
Da Dumi-Dumi: Jam’iyyar Labour Ta Ki Amincewa Da Hukuncin Kotun Ƙararrakin Zabe, Ta Fadi Mataki Na Gaba
Asali: Legit.ng