Yan Bindiga Sun Harbe Jami'an Tsaro da Wata Mata Har Lahira a Benuwai
- 'Yan bindigan da ba a san ko su waye ba sun sake kai hari jihar Benuwai da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya, sun kashe mutum uku
- Rahoto ya nuna maharan sun bindige jami'an tsaron rundunar 'yan sa'kai biyu da wata mata ɗaya a ƙaramar hukumar Logo
- Ƙungiyar 'yan sa'kai ta jihar ta tabbatar da lamarin amma rundunar 'yan sanda ta ce har yanzun rahoto bai riske ta ba
Benue - Wasu miyagun 'yan bindiga da ake kyautata zaton 'yan fashin daji ne sun harbe mutum uku har lahira a ƙauyen Ugba da ke ƙaramar hukumar Logo a jihar Benuwai.
Rahoto ya nuna cewa daga cikin waɗanda 'yan bindigan suka halaka har da jami'an tsaron ƙungiyar 'yan sa'kai ta jihar Benue State Volunteer Guards (BSCVG).
Mazauna 'yankin da lamarin ya faru sun bayyana cewa 'yan bindin sun kashe jami'an BSCVG guda biyu ne a garin Ugba yayin da mutun na uku, wata mata aka harbe ta har lahira a garin Abeda-Shitile.
Jaridar Sunnews ta rahoto cewa mutane da yawa sun ji raunuka daban-daban a harin yayin da maharan suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi da yammacin ranar Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon shugaban ƙaramar hukumar Logo, Terser Agber, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga wakilin jaridar Daily Trust ta wayar salula.
Ya ce 'yan sa'kai biyu, waɗanda tsohon gwamnan jihar, Samuel Ortom ya rushe aikinsu, sun rasa rayuwarsu ne a hannun 'yan bindigan da ba a san ko su waye ba.
Wane mataki jami'an tsaro suka dauka?
Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, jami'an hulɗa da jama'a na ƙungiyar 'yan sa'kai BSCVG, Ahokegh Collins Terkimbi, ya bayyana cewa mutum 2 ne suka rasa rayukansu a harin.
Sai dai a nata ɓangaren, jami'ar hulɗa da jama'a ta hukumar 'yan sanda reshen jihar Benuwai, SP Catherine Anene, ta ce har yanzu hukumar ba ta samu rahoton kai harin ba.
Yanzu-Yanzu: Gobara Ta Tashi a Fitaccen Filin Jirgin Sama a Najeriya, Fasinjoji da Ma'aikata Sun Yi Ta Kansu
Jihar Edo: Wani Magidanci Ya Halaka Matarsa Kan Sabanin Abinci
A wani labarin kuma 'Yan sanda sun kama wani magidanci ɗan shekara 21 bisa zargin kashe matarsa kan saɓanin abinci a jihar Edo.
Da yake hira da 'yan jarida, mutumin ya bayyana cewa sun samu saɓani da matarsa ne saboda ta hana shi abinci bayan kammala girki.
Asali: Legit.ng