Kungiyar CAN A Arewacin Najeriya Ta Soki Ba Da Tallafin Tinubu, Ta Ce Ba Tsari A Ciki
- Kungiyar Kiristoci a Arewacin Najeriya ta soki tsarin ba da tallafi na shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da ake yi a yanzu
- Kungiyar ta shawarci Gwamnatin Tarayya da ta samar da wani tsari mai dorewa na rage talauci da kuma samar da aikin yi ga matasa
- Kakakin kungiyar, Gilbert Jechonia shi ya bayyana haka a yau Juma'a 8 ga watan Satumba a cikin wata sanarwa
FCT Abuja - Kungiyar Kiristoci a Arewacin Najeriya (CAN) ta bayyana cewa talauci ya gigita mutanen Najeriya.
A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a yau ta bakin kakakinta, Gilbert Jechonia ta bukaci shugaba Tinubu da ya samar da hanyar dakile hakan.
Meye kungiyar CAN ke cewa kan Tinubu?
Kungiyar ta na magana ne da yawun jihohin Arewa 19 da kuma babban birnin Tarayya, Abuja, cewar TheCable.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kungiyar ta koka kan yadda farashin kaya ya tashi inda ta ce rashin aikin yi ya jefa matasa aikata laifuka daban-daban.
Sanarwar ta ce:
"Rayuwa ta yi wahala yayin da farashin kayayyaki ya tashi da kuma sufuri yadda talaka ba zai iya samun su ba.
"Akwai mummunan yunwa da talauci a kasa yadda 'yan Najeriya ba sa iya ci da kansu.
"Kasuwanni da dama sun ruguje yayin da rashin aikin yi ya jefa matasa aikata laifuka daban-daban."
Wace shawara CAN din ta bai wa Tinubu?
Kungiyar ta ce a tunaninta wannan tallafi babu abin da zai rage ganin cewa ba zai tabbata ba.
Ta shawarci Gwamnatin Tarayya da ta samar da wani tsari na rage talauci mai dorewa, Head Topics ta tattaro.
Ta kuma kirayi Gwamnatin Tarayya da ma na jihohi da su cika alkawuran da su ka dauka ga al'umma musamman wurin inganta rayuwa da tattalin arziki.
Tinubu zai raba tallafi don rage radadi
A wani labarin, Gwamnatin Tarayya ta sanar da himmatuwarta na bai wa ko wace jiha tallafin Naira biliyan biyar don rage radadi.
Tallafin za a ba da shi ne don rage wa mutane radadin cire tallafin mai shugaban ya yi a watan Mayu yayin kama rantsuwar aiki.
Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno shi ya bayyana haka a Abuja jim kadan bayan kammala taron majalisar tattalin arziki na kasa.
Asali: Legit.ng