"Peter Obi Ya Kusa Zama Shugaban Kasa": Fasto Naomi Tay Bayyana Sabon Wahayi

"Peter Obi Ya Kusa Zama Shugaban Kasa": Fasto Naomi Tay Bayyana Sabon Wahayi

  • Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa a ranar Laraba, 7 ga watan Satumba ta yi watsi da ƙararrakin da aka shigar kan nasarar Shugaba Tinubu a zaɓen da ya gabata
  • Bayan kusan sa'o'i 10 ana zartar da hukunci, alƙalan kotun sun bayyana cewa ƙararrakin da Atiku da Peter Obi suka shigar ba su da makama
  • Amma Atiku na jam'iyyar PDP da Peter Obi na jam'iyyar Labour Party sun yi zargin ba ayi musu adalci ba, inda suka shan alwashin tafiya zuwa kotun ƙoli

Kalabari, jihar Rivers - Fasto Naomi George ta bayyana wani sabon wahayi da ta samu akan Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP) a babban zaɓen 2023.

Fasto Naomi ta bayyana cewa ɗan takarar na Labour Party (LP), nan bada jimawa ba za a bayyana shi a matsayin sabon shugaban ƙasan Najeriya.

Kara karanta wannan

Malamar Da'awa Ta Fadi Cewa Ta Hango Peter Obi Ya Zama Shugaban Najeriya

Fasto Naomi ta fadi sabon wahayi akan Peter Obi
Fasto Naomi ta ce Peter Obi na dab da zama shugaban kasa Hoto: Mr. Peter Obi
Asali: Facebook

Malamar addinin ta bayyana cewa kowane wahayi yana da lokacin tabbatuwarsa.

"Peter Obi zai karɓi mulki": Fasto Naomi

A cewar malamar addinin, lokacin cika wannan sabon wahayin da ta samu ya kusa zuwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Fasto Naomi dai ta bayyana hakan ne a wani rubutu da ta yi a shafinta na Facebook a ranar Alhamis, 7 ga watan Satumban 2023.

A kalamanta:

"Nan bada jimawa ba za a bayyana Peter Obi a matsayin shugaban ƙasan Najeriya. Tinubu zai sauka domin Obi ya karɓi ragamar mulkin ƙasar nan."
"Amma abun takaicin shi ne ba na ganin sabuwar Najeriya ('Sabuwar Najeriya' na ɗaya daga cikin kalaman da Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra yake amfani da su wajen yaƙin neman zaɓe). Abin da na ke gani kawai shi ne ci baya, shan wuya da baƙin ciki. Kalmar ubangiji ba za ta taɓa sauyawa ba."

Kara karanta wannan

Hukuncin Kotu: An Bayyana Wani Muhimmin Dalili Da Zai Sanya Shugaba Tinubu Ya Cigaba Da Nasara Akan Atiku Da Peter Obi

Jam'iyyar LP Ta Rasa 'Yan Majalisa

A wani labarin na daban kuma, jam'iyyar Labour Party (LP) wacce Peter Obi ya yi takara a cikinta, ta rasa ƴan majalisa uku a kotun zaɓe.

Jam’iyyar hamayyar ta lashe kujerun majalisar wakilai fiye da 20 a zaɓen bana, amma sannu a hankali kotu ta na zaftare mata ƴan majalisa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng