Tsohon Shugaban Kasa Buhari Ya Yi Ta'aziyyar Rasuwar Sheikh Giro Argungu

Tsohon Shugaban Kasa Buhari Ya Yi Ta'aziyyar Rasuwar Sheikh Giro Argungu

  • Muhammadu Buhari, tsohon shugaban ƙasa ya yi jimamin rasuwar fitaccen Malamin Musulunci, Sheikh Abubakar Giro
  • A saƙon ta'aziyyar da ya fitar ranar Alhamis, Buhari ya bayyana rasuwar Malamin da babban rashi ga Najeriya da Musulunci
  • Ya kuma miƙa ta'aziyya ga iyalansa da mabiyansa kana ya yi Addu'ar Allah ya sa shi a gidan Aljannah

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya aike da saƙon ta'aziyya biyo bayan rasuwar fitaccen Malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Abubakar Giro Argungu.

Muhammadu Buhari ya yi jimamin rasuwar Malamin ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu, ya fitar ranar Alhamis, 7 ga watan Satumba, 2023.

Muhammadu Buhari ya yi ta'aziyyar rasuwar Sheikh Abubakar Giro.
Tsohon Shugaban Kasa Buhari Ya Yi Ta'aziyyar Rasuwar Sheikh Giro Argungu Hoto: Buhari Sallau
Asali: UGC

Buhari ya ayyana rasuwar Sheikh Abubakar Giro a matsayin wani babban rashi ga Najeriya da duniyar Musulunci baki ɗaya, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Giro Argungu: Atiku Abubakar Ya Mika Sakon Ta'aziyyarsa Ga Iyalan Malamin

"Ina miƙa ta'aziyya ga iyalansa da sauran masoyansa," in ji tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Sheikh Abubakar Giro ya kasance babban jigo mai muhimmanci ga rayuwarmu da ƙasar nan. A tsawon rayuwarsa ya tsaya tsayin daka wajen tabbatar da kyawawan dabi'un Musulunci."
"Marigayin yana kuma ba da gudummuwa wajen gina al'umma ta gari ta hanyar kalamansa da kuma ayyukansa. Allah mai girma da ɗaukaka ya masa rahama ya sa shi a gidan Aljannatul Firdausi."

Shikh Abubakar Abdullahi Giro Argungu ya rasu ne jiya Laraba da yammaci bayan fama da gajeruwar jinya a birnin Kebbi, babban birnin jihar Kebbi.

Malamin yana ɗaya daga cikin manyan Malumman ƙungiyar jama'atul Izalatil Budi'a Wa Ikamatis Sunnah watau JIBWIS a taƙaice.

An yi jana'izar Sheiƙh Giro a Kebbi

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa a yau Alhamis aka yi wa Marigayin Jana'iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a jihar Kebbi.

Kara karanta wannan

"Ku Taimaka Mana" Ministan Tinubu Ya Roƙi Yan Najeriya Alfarma 1 Tak, Ya Ce Akwai Matsala

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi ta'aziyyar rasuwar Sheikh Abubakar Giro, tare da Addu'ar Allah ya gafarta masa, kamar yadda Daily Post ta rahoto.

Atiku Abubakar Ya Yi Jimamin Rasuwar Sheikh Giro Argungu

A wani labarin kuma Dan takarar shugabancin ƙasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya miƙa saƙon ta'aziyyar Sheikh Abubakar Giro Argungu.

Atiku ya ce Sheikh Giro na daga cikin manyan-manyan malaman addinin Musulunci da ake girmamawa a Najeriya da Yammacin Afrika baki daya, saboda irin gudummawar da ya ba da.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262