Matsalar Tsaro: "Muna Bukatar Addu'arku" Ministan Tsaro Ya Roki Yan Najeriya
- Ministan tsaron tarayya, Badaru Abubakar, ya roƙi 'yan Najeriya su taimaka masa da addu'a domin magance matsalar tsaro
- Badaru, tsohon gwamnan Jigawa ya karɓi bakuncin tawagar wakilai daga jiharsa karkashin gwamna Umar Namadi
- Gwamnan ya bayyana cewa sun kai masa wannan ziyara ne domin taya shi murna da kuma yi masa addu'ar samun nasara
FCT Abuja - Ministan Tsaro, Abubakar Badaru, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da yi wa gwamnati mai ci addu’a, musamman masu rike da mukaman tsaron kasa.
Badaru ya yi wannan kira ne yayin da ya karɓi bakuncin wakilan jiharsa ta Jigawa karkashin jagoranci Gwamna Malam Umar Namadi a ofishinsa da ke Abuja.
Ministan ya ce duba da sarƙaƙiyar da ke tattare da sha'anin tsaron Najeriya da sauran bangarorin ci gaban ƙasa, "Ba abin da muka fi buƙata wanda ya wuce Addu'a."
A cewarsa, duk da cewa aikin da ke gabansu ba ƙarami bane kuma yana da yawa, amma sun kuduri aniyar shawo kan kalubalen baki ɗaya, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Saboda haka, Badaru, tsohon gwamnan jihar Jigawa ya roƙi 'yan Najeriya su mara musu baya ta kowane fanni musamman addu'o'i domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Me ya sa wakilan Jigawa suka ziyarci Badaru?
Sarakuna, Malaman addini da manyan 'yan kasuwa na cikin tawagar wakilan da gwamna Ɗan Modi ya jagoranta suka kai wa Ministan ziyara a Ofishinsa.
Da yake jawabi tun farko, gwamna Namadi ya ce shi da sauran wakilan sun tako har Ofis ne domin su taya Ministan murna kuma su tabbatar masa da goyon baya 100%.
Tribune ta rahoto Namadi na cewa:
Shugaban Majalisar Dattawa Ya Magantu Kan Hukuncin da Kotun Zabe Ta Yanke, Ya Fada Wa Atiku da Obi Mafita
"Ba murna kaɗai muka zo taya ka ba, harda addu'a. Mun san yadda ka yi nasara a matsayinka na gwamnan jiharmu, muna kuma yi maka addu’ar samun nasara ko fiye da haka a wannan sabon aikin na Ministan Tsaro.”
Ya kuma tunatar da ministan cewa ‘yan Najeriya na sa ran zai yi wa kasa hidima tare da magance matsalar tsaro, inda ya kara da cewa “da zarar ka yi haka, ya shafi kowane bangare na kasa."
Atiku da Peter Obi Sun Lashi Takobin Daukaka Kara Zuwa Kotun Koli
A wani labarin na daban Atiku Abubakar da Peter Obi sun yi fatali da hukuncin Kotun sauraron ƙarar zaben shugaban ƙasa, zasu ɗaukaka ƙara.
Jim kaɗan bayan yanke hukunci ranar Laraba, Lauyoyin Atiku da Peter Obi sun tabbatar da cewa zasu kalubalanci hukuncin a Kotun Ƙoli.
Asali: Legit.ng