An Cigaba da Biyan Mahaifinsu Albashi da Ya Rasu, Matashi Ya Maidawa Gwamna Kudin

An Cigaba da Biyan Mahaifinsu Albashi da Ya Rasu, Matashi Ya Maidawa Gwamna Kudin

  • Abba Kabir Yusuf ya hadu da wani matashi a Kano mai gaskiya da ya ki taba dukiyar da ba ta shi
  • Yusuf Sulaiman Sumaila ya maida N328,115.75 da aka tura cikin asusun mahaifinsu da ya rasu
  • Mai girma Gwamnan ya ji dadin yadda wannan mutumi ya dawo da dukiyar da ba hakkin magada ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya jinjinawa wani matashi, Yusuf Sulaiman Sumaila wanda ya nuna gaskiya da bin doka.

Wannan Bawan Allah ya dauki albashin da aka biya mahaifinsu da ya rasu, sai ya maida cikin baitul-malin jihar Kano domin ba hakkinsa ba ne.

Mai taimakawa Gwamnan Kano a dandalin sada zumunta na zamani, Abdullahi Ibrahim ya bayyana haka a shafin X da aka fi sani da Twitter.

Kara karanta wannan

Matashi Ya Dawo Da Albashin Da Gwamnati Ta Rika Biyan Mahaifinsa Bayan Ya Rasu a Kano, Gwamna Ya Yi Masa Wani Muhimmin Abu

Gwamna Abba Kabir Yusuf
Yusuf Sulaiman Sumaila tare da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf
Asali: Twitter

Gwamnatin Kano ta cigaba da biyan shi albashi

Malam Abdullahi Ibrahim yake cewa a Oktoban 2022 mahaifinsu ya rasu, amma sai gwamnati ta cigaba da biyansa albashi har Agusta na 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ganin haka sai Yusuf Sulaiman Sumaila ya tattara kudin ya maida cikin asusun gwamnatin jihar, adadin dukiyar da aka maida shi ne N328,115.75.

Ga Yusuf Sulaiman Sumaila ga Abba Gida Gida

Shi kuwa a bangarensa, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya gana da Yusuf Sulaiman Sumaila a gidan gwamnati, ya kuma yaba masa saboda irin gaskiyarsa.

Gwamnan ya ji dadin yadda matashin ya sanar da hukuma domin a daina biyan marigayin albashi tun da Ubangiji ya dauki ransa a shekarar bara.

Ya aka yi ya hadu da Gwamna?

Da Legit.ng Hausa ta yi magana da Abubakar Ibrahim a kan yadda hakan ta faru, sai ya ce Yusuf Sumaila ne ya tuntube shi a kafar Twitter kwanaki.

Kara karanta wannan

Tsadar Fetur: Yadda Abba Gida Gida Ya Yi Rabon Kayan Tallafi ga Mata da Manoma

Matashin ya sanar da shi ya na bukatar ganin gwamna domin ya maida kudin da ke hannunsu a cikin lalitar gwamnati, sai hadimin ya yi masa hanya.

Mai bada shawarar ya ce an yi zaman ne daga wannan Bawan Allah sai gwamnan a gidan gwamnati.

An raba kayan tallafi a Kano

Mu na da labari Gwamnatin Kano ta raba buhunan shinkafa fiye da 270,000 da kananan buhunan masara 160, 000 a sakamakon tsadar rayuwa.

A makon nan Gwamnan Kano da aka fi sani da Abba Gida Gida ya ba manoma da matan kauye da kayan aikin gona da dabbobi da za su rika kiwo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng