Wani Mutum Da Ya Fara Sana’ar Ayaba Da Kasa Da N100k Ya Gina Gida 3, Yana Shirin Fadin Sirrin
- Wani dan Najeriya ya nunawa mutane gida na uku da yake ginawa a yanzu haka bayan ya fara sana'ar siyar da soyayyen ayaba
- Mutumin ya bayyana cewa ya zuba kasa da N100k cikin sana'ar shekaru hudu da suka gabata kuma ya samu riba sosai
- Yan Najeriya da dama da ke neman hanyoyin dogaro da kai sun ce suna sha'awar jin sirrin kasuwancinsa
Wani hazikin dan Najeriya da ke sana'ar siyar da soyayyen ayaba ya nunawa duniya gidan da yake ginawa.
Mutumin mai suna @adegbengaolusegun ya ce ginin shine gida na uku da ya gina tun bayan da ya fara sana'ar siyar da soyayyen ayaba.
Yadda wani mutum ya fara sana'a da kasa da N100k
Mutane da dama da suka kalli bidiyonsa a TikTok sun nuna sha'awar son jin labarinsa lokacin da ya bayyana cewa ya fara sana'ar da kasa da N100k. Ya yi alkawarin fadawa mutane sirrin nasarar da ya samu a sana'ar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Wani bidiyo ya nuna mutane da dama suna aiki a ma'aikatarsa yayin da suke bare bawon danyen ayaba.
Da yake nuna aikin ginin da yake yi, mutumin ya ce an kai linta cikin kasa da kwana shida. Ya kara da cewar za a kammala ginin gidan cikin wata daya.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi tambayoyi kan kasuwanci
Ochowechi ya ce:
"Dan uwa, don Allah ta yaya zan iya fara wannan kasuwancin yallabai."
awaomaka ta yi mamaki:
"Menene dalilin da yasa baka fada a nan ba?"
@ibrahim adams ya ce:
"Dan uwa don Allah ina sha'awa don bana so na bar duniyar nan ba tare da na ginawa yarana gida ba."
adewunmi693 ya ce:
"Da ace na gan ka da dadewa da yanzu na mallaki gidan kaina."
Matashi ya gargadi maza masu tafiya turai suna barin matansu a gida
A wani labarin, wani dan Najeriya mai suna @odogwukiwi a TikTok ya aika gagarumin gargadi kan dabi'ar barin mata a gida don tafiya wata kasar.
A cikin bidiyon, Odogwukiwi ya nuna damuwarsa, yana mai bayyana cewa yana da matukar hatsari barin matar mutum a gida yayin da ya shi zai tafi turai.
Asali: Legit.ng