Matashi Ya Mayar Da Albashin Da Aka Rika Biyan Mahaifinsa Bayan Ya Rasu a Kano
- Wani matashi a jihar Kano ya nuna halin tsoron Allah inda ya dawo da albashin da gwamnati ta riƙa biyan mahaifinsa bayan ya rasu
- Yusuf Sulaiman Sumaila ya dawo da albashin N328,115.75 da gwamnati ta biya mahaifinsa bayan rasuwarsa
- Gwamna Abba Kaɓir Yusuf ya aike da saƙon gayyata na musamman ga Sulaiman inda ya yaba masa kan halin dattakon da ya nuna
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yaba wa wani matashi mai suna, Yusuf Sulaiman Sumaila, bisa dawo da albashin da aka riƙa biyan mahaifinsa bayan ya rasu.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin gwamnan, Abdullahi Ibrahim, ya fitar a shafinsa na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter).
Mahaifin Sumaila ya rasu ne a watan Oktoban 2022 amma gwamnati ta cigaba da biyansa albashi har zuwa watan Agustan 2023.
Sai dai, matashin bayan ya lura da abin da ke faruwa sai ya dawo da albashin ga gwamnatin jihar inda ya sanar da ita cewa mahaifinsa ya rasu shekara ɗaya da ta gabata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matashin ya dawo da tsabar kuɗi har N328,115.75 ga gwamnatin jihar waɗanda aka riƙa biyan mahaifinsa bayan ya rasu.
Wani ɓangare na sanarwar na cewa:
"Yusuf ya bayyana cewa gwamnatin jiha ta cigaba da biyan albashin marigayin mahaifinsa a asusunsa bayan rasuwarsa a watan Oktoban 2022 har zuwa watan Agustan 2023, lokacin da ya buƙaci a daina biyan kuɗin a hukumance."
"Yusuf ya kuma buƙaci ya dawo da jimillar kuɗi N328,115.75 da aka biya ga gwamnatin jihar, wanda hakan ya sanya gwamna da kansa ya gayyace shi zuwa ofishinsa domin ya gode masa."
Gwamna Abba ya yaba wa matashin
Gwamna Abba ya yaba bisa wannan halin dattako da matashin ya nuna inda ya buƙaci sauran matasa su yi koyi da shi wajen yin riƙo da amana.
"Gobe Ka Kara": Matar Aure Ta Kwarawa Dan Cikinta Tafasashshen Ruwan Zafi Bayan Ya Aikata Wani Abu 1
Sanarwar ta cigaba da cewa:
"Da yake na sa jawabin, gwamna Abba ya yaba wa Yusuf bisa wannan karamcin da ya yi, inda ya yi kira ga sauran matasa da su yi koyi da shi wajen nuna halin gaskiya."
Abba Ya Yi Rabon Kayan Tallafi
A wani labarin kuma, gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya yi rabon kayan tallafi ga mata da manoma.
Gwmanan ya yi rabon tallafin ne bayan ya karbi kasonsa daga gwamnatin tarayya na tallafin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur.
Asali: Legit.ng