Kotu Ta Tabbatar Da Nasarar Sanatan Jam'iyyar APC Na Oyo Ta Kudu

Kotu Ta Tabbatar Da Nasarar Sanatan Jam'iyyar APC Na Oyo Ta Kudu

  • Kotun sauraron ƙarar zaɓen sanatan Oyo ta Kudu ta ba sanatan jam'iyyar All Progrrssives Congress (APC) nasara
  • Kotun ta tabbatar da nasarar Sanata Sharafadeen Abiodun Alli a zaben sanatan na Oyo ta Kudu da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu
  • Kotun zaɓen ta yi fatali da ƙarar da ɗan takarar jam'iyyar PDP ya shigar yana ƙalubalantar nasarar Sanata Sharafadeen a zaɓen

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Oyo - Kotin sauraron ƙarar zaɓen sanatan Oyo ta Kudu ta tabbatar da nasarar sanatan jam'iyyar All Progressives Congress, Sanata Sharafadeen Alli, cewar rahoton Tribune.

Kotun a hukuncinta ranar Laraba a birnin Ibadan, ta yi watsi da ƙarar da ɗan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Cif Joseph Tegbe, ya shigar inda yake ƙalubalantar sakamakon zaɓen wanda ya samar da Alli a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Jam’iyyar Labour Ta Ki Amincewa Da Hukuncin Kotun Ƙararrakin Zabe, Ta Fadi Mataki Na Gaba

Kotu ta tabbatar da nasarar sanata Sarafadeen
Kotu ta tabbatar da nasarar Sanata Sarafadeen Alli a zaben Sanatan Oyo ta Kudu Hoto: Sharafadeen Abiodun Alli
Asali: Facebook

Alli a zaɓen wanda aka gudanar a rumfunan zaɓe sama da 2000 a ƙananan hukimomi tara, ya samu ƙuri'u 111,513 yayin da Tegbe ya samu ƙuri'u 92,481.

A lokacin sauraron ƙarar, Tegbe ya kira shaidu 32 ciki har da kansa domin tabbatar da cewa zaɓen an tafka maguɗi a cikinsa sannan ba a gudanar da shi bisa tanadin sabuwar dokar zaɓe ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wane hukunci kotu ta yanke?

A yayin yanke hukunci, kotun ta bayyana cewa sa hannun da yawa daga shaidun waɗanda suka gabatar da kansu a matsayin wakilan PDP a rumfunan zaɓe, ba su yi daidai da sa hannun da ke jikin takardun da a ka sanya wa hannu a rumfunan zaɓe ba da kuma takardun da ke ɗauke da bayanan su.

A cewar kotun, ɗaya daga cikin shaidun lokacin da aka titsiye shi da tambayoyi, ya bayyana cewa ba shi ba ne ya yi bayanin da aka ce ya yi akan rantsuwa sannan sa hannun da ke jikin bayanin ba na sa ba ne.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Peter Obi Ya Yi Nasara Akan Shugaba Tinubu Da Shettima a Kotun Zabe

Kotun ta bayyana cewa shaidun ba su bayyana katin shaida ba wanda zai nuna cewa sun yi aiki a matsayin wakilan akwatu a ranar zaɓen, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Kotun ta kuma bayyana cewa masu shigar da ƙarar sun kasa kawo gamsassun hujjoji waɗanda za ta yarda da su.

Kotun ta bayyana cewa:

"Masu shigar da ƙarar sun kasa kawo hujja gamsasshiya, mai ƙarfi wacce za a yarda da ita kan sakamakon zaɓen da INEC ta bayyana."

Peter Obi Ya Yi Nasara Kan Tinubu a Kotu

A wani labarin kuma, kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa, ta ƙi amincewa da wasu buƙatu biyu na jam'iyyar APC da Shugaba Tinubu.

Kotun ta yi fatali da ƙorafin zaman Peter Obi halastaccen mamban jam'iyyar Labour Party da batun ƙin haɗa ƙararsa tare da ta Atiku Abubakar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng