Da Gaske Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo Ya Mutu? Hadiminsa Ya Yi Martani

Da Gaske Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo Ya Mutu? Hadiminsa Ya Yi Martani

  • Kehinde Akinyemi, kakakin tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya yi watsi da ikirarin cewa ubangidansa ya mutu
  • Akinyemi ya ce jita-jitan da ke yawo na mutuwar tasa karya ne domin Obasanjo na cikin koshin lafiya kuma yanzu haka yana wajen kasar
  • Ya bayyana hakan ne yayin da yake martani ga wabi bidiyon WhatsApp da ya yadu wanda ke ikirarin cewa tsohon shugaban Najeriyan ya mutu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Ogun - Kehinde Akinyemi, mai magana da yawun tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya yi martani ga wani bidiyo da ke ikirarin cewa ubangidansa ya mutu.

A cewar Dubawa, wani bidiyon WhatsApp da ke ikirarin cewa Obasanjo ya mutu ya yadu a ranar Talata, 5 ga watan Satumba, 2023.

Hadimin Obasanjo ya ce tsohon shugaban kasar na nan da ransa
Da Gaske Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo Ya Mutu? Hadiminsa Ya Yi Martani Hoto: Goodluck Jonathan
Asali: Facebook

Bidiyon WhatsApp ya yi ikirarin Obasanjo ya mutu

Kara karanta wannan

Bidiyoyi Da Hotuna Sun Bayyana Yayin da Ganduje, Keyamo, Bala Mohammed Da Sauransu Ke Likimo a Kotun Zaben Shugaban Kasa

Dandalin mai binciken gano gaskiya ya ce an yi wa bidiyon take ne da harshen faransa - DÉCÈS DE L’ANCIEN PRÉSIDENT DU NIGERIA OLUSHEGUN OBASANJO” wato ma'ana "MUTUWAR TSOHON SHUGABAN KASAR NAJERIYA OLUSEGUN OBASANJO."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kuma, an yi kuskure wajen rubuta sunan tsohon shugaban kasar inda aka sa Olushegun a taken bidiyon.

Bidiyon mai tsawon sakan 12 na dauke da taken RIP wanda ke nufin Allah ya ki kanka, rubuce baro-baro a kan hotunan Obasanjo da aka hada.

An gano cewa wani mai amfani da TikTok, Wazobia.fm ne ya wallafa bidiyon a ranar Talata, 5 ga watan Satumba kuma mutum 202 ne suka sake yada shi.

An kuma lura cewa an rufe sashin sharhi a wannan wallafa ta TikTok.

An kuma tattaro cewa mai amfani da shafin na TikTok ya kware sosai wajen yada bidiyoyi kan mutuwar shahararrun mawaka, yan fim da fastocin Najeriya, da dai wannan sautin.

Kara karanta wannan

Hukuncin Kotu: Rabaran Mbaka Ya Gaya Wa Shugaba Tinubu Ya Shirya Barin Ofis? Gaskiya Ta Bayyana

Obasanjo bai mutu ba

Da yake martani kan rade-radin mutuwar Obasanjo, Akinyemi ya ce tsohon shugaban Najeriyan na nan lafiya kuma a yanzu haka yana wajen kasar.

"Yana a wajen kasar! Tanzania ko Kenya zuwa safiyar nan."

Dama Na San Bai San Tattalin Arziki ba – Obasanjo Ya Kuma Ragargazar Buhari

A wani labarin kuma, mun ji cewa Olusegun Obasanjo ya mulki Najeriya a lokacin mulkin soja da na farar hula, ya yi shekaru fiye da 10 a kan karaga, ya san kan kasar nan.

A wata hira ta musamman da ya yi da The Cable, Cif Olusegun Obasanjo ya yi maganar shugabanci, lantarki, tattalin arziki da dai sauransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng