Kotu Ta Soke Zaben Sanatan APC Na Kogi Ta Gabas, Jibril Isah

Kotu Ta Soke Zaben Sanatan APC Na Kogi Ta Gabas, Jibril Isah

  • Kotun sauraron ƙarar zaɓen sanatan Kogiɓta Gabas ta soke zaɓen sanatan jam'iyyar APC, Jibril Isah
  • Kotun ta amince da buƙatar da ɗan takarar jam'iyyar PDP, Dakta.Victor Adoji ya shigar na neman a soke zaɓen Isah
  • Mai shari'a K.A Orjiako ya umarci hukumar INEC da ta gudanar da zaɓen cike gurbi a rumfunan zaɓe 94 domin tantance wanda ya yi nasara

Jihar Kogi - Kotun sauraron ƙarar zaɓen Sanatan Kogi ta Gabas mai zamanta a Lokoja, ta soke zaɓen sanatan jam'iyyar All Progressive Congress (APC), Sanata Jibrin Isah, bisa dalilin cewa an soke zaɓe a wasu rumfunan zaɓe 94.

Shugaban kotun, mai shari'a K.A. Orjiako, wanda ya yanke hukuncin kan ƙarar da Dakta Victor Adoji, ɗan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya shigar, ya amince da buƙatun da Adoji ya nemi kotun ta yi masa, cewar rahoton Tribune.

Kara karanta wannan

Atiku, Obi Da Tinubu: Jigon PDP Ya Ce Bai Dace Kotu Ta Ayyana Wanda Ya Yi Nasara Ba, Ya Fadi Abinda Ya Kamata a Yi

Kotu ta soke zaben sanatan Kogi ta Gabas
Kotu ta soke nasarar.Sanata Jibril Isah Hoto: @Shaibu_AO
Asali: Twitter

Adoji ta hannun lauyansa, Mista Johnson Usman (SAN), ya ƙalubalanci nasarar Isah kan dalilin cewa an soke zaɓe a wasu rumfunan zaɓe inda yawan katin zaɓen da aka ƙarba, ya wuce adadin yawan ƙuri'un da Isah ya samu nasara a kansa da su.

Adoji ya buƙaci kotun da ta soke zaɓen Isah sannan ta bayar da umarnin sake zaɓen cike gurbi a rumfuna 94 da abun ya shafa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wane hukunci kotun ta yanke?

Da yake yanke hukuncinsa kan ƙarar, mai shari'a K.A. Orjiako ya amince da bayanan da lauyan Adoji ya yi, sannan ya soke nasarar Isah tare da bayar da umarnin janye satifiket ɗin lashe zaɓe da aka ba shi.

A kalamansa:

"Tun da katin ƙada ƙuri'a da aka karɓa a rumfunan zaɓe 94 yawansu shi ne 59,730, yayin da tazarar nasarar ita ce ƙuri'u 26,922, kamata ya yi baturen zaɓen ya sanar da zaɓen a matsayin wanda bai kammalu ba."

Kara karanta wannan

Manya-manyan Bukatu 5 Da Peter Obi Ya Mikawa Kotu Kan Shari'arsa Da Bola Tinubu

"A saboda haka wannan kotun ta amince da buƙatun da masu shigar da ƙara suka nema, sannan ta jingine satifiket ɗin lashe zaɓe da aka ba Jibril Isah."
"Wannan kotun ta kuma umarci INEC ta gudanar da zaɓen cike gurbi a rumfunan zaɓen da abun ya shafa inda ba a yi zaɓe ba ko aka soke zaɓen domin samun wanda ya yi nasara a zaɓen."

Kotun ta kuma umarci INEC ta gudanar da zaɓen cike gurbi a rumfunan zaɓe 94 da abun ya shafa, rahoton Voice of Nigeria ya tabbatar.

Da Wuya Kotu Ta Iya Yanke Hukunci Ranar Laraba, Bulama

A wani labarin na daban kuma, sanannen lauya Bulama Bukarti ya yi magana kan yiwuwar.kotun zaɓen shugaban ƙasa ta iya yanke hukuncinta a ranar Laraba, 6 ga watan Satumba.

Bulama ya bayyana cewa yajin aikin gargaɗi da ƙungiyar ƙwadago ke yi, ka iya hana kotun yanke hukuncinta a ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng