Jami'an DSS Sun Kama Masu Karkatar da Tallafin Gwamnati a Jihar Nasarawa

Jami'an DSS Sun Kama Masu Karkatar da Tallafin Gwamnati a Jihar Nasarawa

  • Hukumar DSS ta kama ma'aikatan gwamnati bisa zargin wawure wasu kayan tallafin da FG ta samar domin raba wa yan Najeriya
  • Mai magana da yawun DSS, Peter Afunanya, ya ce a halin yanzu an kama wasu a jihar Nasarawa kuma an kwato kayan da suka ɗiba
  • Ya yi kira ga ɗaukacin 'yan Najeriya su kai rahoton masu aikata wannan laifi ga hukumomin tsaro domin ɗaukar mataki

FCT Abuja - Jami'an hukumar tsaron farin kaya (DSS) sun kama wasu ma'aikatan hukumar ba da agajin gaggawa ta jiha da ke karkatar da kayan tallafin da ake raba wa talakawa.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa dakarun DSS sun kama jami'an ne bisa zargin wawure kayayyakin tallafin raɗe raɗaɗi da gwamnati ke raba wa mutane bayan cire tallafin man fetur.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Miyagun 'Yan Fashi Sun Kai Kazamin Hari Yankuna Uku a Babban Birnin Jihar PDP

Jami'an hukumar DSS.
Jami'an DSS Sun Kama Masu Karkatar da Tallafin Gwamnati a Jihar Nasarawa Hoto: dailytrust

Wasu daga cikin waɗanda ake zargin sun shiga hannun DSS ne a fitacciyar ƙasuwar Lafiya, babbam birnin jihar Nasarawa inda suke sayar da kayayyakin.

Daga cikin waɗanda aka kama sun haɗa da jami'an hukumar bada agaji ta jihar Nasarawa (NASEMA) da wasu masu taimaka musu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mai magana da yawun hukumar DSS ta ƙasa, Peter Afunanya, ne ya tabbatar da kama mutanen ga manema labarai a babban birnin tarayya Abuja.

Ya ƙara da cewa a halin yanzun jami'ai sun kwato wasu daga cikin kayayyakin tallafin da waɗanda ake zargi suka wawure.

Wane mataki za a ɗauka kan waɗanda suka shiga hannu?

Mista Afunanya ya yi ƙira ga ɗaukacin 'yan Najeriya waɗanda ke da bayanan sirri kan karkatar da tallafin, su garzaya su kai rahoto ga hukumomin tsaro domin ɗaukar mataki.

Kara karanta wannan

Shari'ar Atiku, Obi Da Tinubu: Jami'an Tsaro Sun Fitar Da Muhimmin Gargaɗi Gabanin Yanke Hukunci

"Hukumar DSS ta samu rahoto daga gwamnatocin jihohi dangane da karkatarwa ko sayar da tallafin da aka ware domin raba wa 'yan Najeriya."
"Bisa haka hukumar ta fara bincike kuma ta baza komarta kan lamarin wanda sakamakon haka jami'ai suka kwato wasu kyayyakin tallafin kuma suka damƙe waɗanda ake zargi."

- Peter Afunanya.

Ya bayyana cewa a halin yanzun jami'an sun fara bincike domin gano masu wawure tallafin a sauran jihohin Najeriya, kamar yadda Vanguard ta tattaro.

Gwamnan Delta Ya Nada Abokin Adawarsa Na NNPP a Matsayin Hadimi

A wani rahoton kuma Gwamnan jihar Delta na jam'iyyar PDP ya naɗa sabbin masu ba shi shawara ta musamman guda 9 cikk harda abokan hamayya.

Sakataren gwamnatin jihar Delta (SSG), Kingsley Emu, shi ne ya tabbatar da haka ga manema labarai a Asaba, babban birnin jihar Delta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262