“Su Na Samun Kudade”: Wata Budurwa Ta Je Hutu Ingila Yayin Da Ga Yadda Ake Samun Kudi A Sauki

“Su Na Samun Kudade”: Wata Budurwa Ta Je Hutu Ingila Yayin Da Ga Yadda Ake Samun Kudi A Sauki

  • Wata budurwa da ta je hutu kasar Ingila ta bayyana irin yadda ta ga ma’aikatansu su ke hutawa da samun kudi
  • Budurwar mai suna Judith Samuel ta ce ma’aikata a can su na aiki ne na kankanin lokaci tare da samun makudan kudade
  • Ta kwatanta da Najeriya inda ta ce ana aiki kwanaki shida a mako amma kuma kudin bai taka kara ya karya ba

Wata budurwa na tunanin dawowa Najeriya bayan ta je Ingila don yin hutu na dan karamin lokaci.

Budurwar mai suna Judith Samuel ta ce ta fahimci aiki a Ingila ba wahala kamar na Najeriya, Legit.ng ta tattaro.

Bidiyon wata budurwa ya yadu inda ta je hutu Ingila
Wata Budurwa Ta Je Hutu Ingila Ta Sha Mamaki Ganin Yadda Ake Samun Kudi a Sauki. Hoto: TikTok/@imjudy31 and Getty Images/Aaron Foster.
Asali: UGC

Meye budurwar ta ce kan Ingila?

Judith ta ce mutane a kasar Ingila su na aiki ne kwanaki hudu kacal a mako idan aka kwatanta da Najeriya da mutane ke aiki har kwanaki shida.

Kara karanta wannan

Satar Amfani: Manoma Sun Bayyana Yadda Su Ke Biyan Kudi Da Kwana A Gona Don Kare Amfaninsu, Sun Koka Kan Yawan Sata

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ce zuwanta Ingila ya bude mata ido da sanin cewa mutanen kasar na aiki na kankanin lokaci kuma su samu makudan kudade.

Judith ta rubuta a TikTok kamar haka:

“Na je Ingila don yin hutu amma abin da na gani ya ba ni mamaki, mutanen nan su na kwashe kudade, anya zan dawo Najeriya kuwa? Ku na samun kudade.”

Ku kalli bidiyon budurwar a kasa:

Mutane da dama sun yi martani inda kowa ke fadin albarkacin bakinsa kan maganar budurwar.

@Olly Okocha:

"Kenan kwanaki hudu a mako shi ne sa’o’i 12 ai babu sauki shi yasa su ka ba da kwanaki uku hutu.”

@Trillionaire_Presh:

"Don Allah an baki izini na baki ko kuma kin je ta wata hanya ce?”

@baguzu:

"Gaskiyar ki, idan mutum ya yi karin aiki bayan sa’o’i 10 kana aiki ne ga ofishin haraji na gwamnati.”

Kara karanta wannan

'Wike Zai Kare a Gidan Yari', Wanda Aka Rusawa Gini Ya Sha Alwashin Shiga Kotu

@Gbolagunte:

"Kafin mutum ya samu damar zuwa hutu a wanna Najeriya ta mu, tabbas ba shi da matsala ko kadan.”

Budurwa Ta Fadi Kyautar Saurayinta Ya Bata A Shekaru 11

A wani labarin, wata budurwa ta wallafa wani faifan bidiyo inda ta bayyana kyautar da saurayinta ya taba mata tsawon lokacin da su ka kwashe su na soyayya.

Budurwar ta ce abin mamaki ita kam ba ta yi sa'a ba domin buroshin goge hakora da safa da kuma man kai kawai ya bata matsayin kyauta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.