'Yan Sanda Sun Kubatar Mutane Uku Daga Hannun 'Yan Bindiga a Kaduna

'Yan Sanda Sun Kubatar Mutane Uku Daga Hannun 'Yan Bindiga a Kaduna

  • Dakarun 'yan sanda sun samu nasarar ceto mutane 3 da yan bindiga suka sace a ƙaramar hukumar Zariya
  • Kakakin rundunar 'yan sandan Kaduna, ASP Manir Hassan, ya ce ana zargin mayaƙan wani hatsabibin ɗan bindiga suka kitsa harin
  • Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan gwamna Uba Sani ya ɗauki sabbin 'yan banga 7,000 a Kaduna

Kaduna - Rundunar 'yan sanda reshen jihar Kano ta ceto mutum 3 waɗanda miyagun 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a yankin ƙaramar hukumar Zariya.

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar, ASP Manir Hassan, ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya fitar, kamar yadda Channels tv ta rahoto.

Jami'an rundunar yan sanda sun kwato mutane a Kaduna.
'Yan Sanda Sun Kubatar Mutane Uku Daga Hannun 'Yan Bindiga a Kaduna Hoto: channels
Asali: UGC

Ya ce dakarun 'yan sanda sun samu nasarar kubutar da mutanen ne yayin da suka fita sintiri a kan titin Kuriga zuwa Wusasa, duk a yankin Zariya.

Kara karanta wannan

Shiri Ya Yi Kyau: Jami'an Yan Sanda Sun Fatattaki 'Yan Bindiga a Arewacin Najeriya, Sun Ceto Mutane Masu Yawa

Yadda 'yan banga suka ba da gudummuwa

A cewarsa, sun samu wannan nasara ne tare da haɗin guiwar ƙungiyar 'yan banga, waɗanda suka samu bayanan sirri kuma suka kai ɗauki cikin jeji.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kakakin rundunar 'yan sandan ya ƙara da bayanin cewa bayan samun sahihan bayanai na sirri, 'yan bangan sun kai ɗauki cikin jejin, kuma hakan ya tilasta wa 'yan bindigan guduwa.

Ya ce bisa dole yan bindigan da suka yi garkuwa da mutanen uku suka tsere zuwa cikin daji domin tsira rayuwarsu kuma suka bar mutanen 3 da suka sace.

'Yan sanda sun kano masu hannu a harin

Haka zalika ya yi bayanin cewa ana zargin mayaƙan ƙasurgumin ɗan bindigan nan, Marigayi Isah Ɗanwasa ne suka kitsa yin garkuwa da mutanen, Dailypost ta tattaro.

Bayanai sun nuna cewa hatsabibin ɗan bindigan, Isa Ɗanwasa, ɗan asalin wani yanki ne a ƙaramar hukumar Zariya da ke cikin jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Abin Mamaki: Wata Akuya Ta Haifi Rabi Mutum Rabi Akuya a Wata Jihar Arewa, Bidiyonta Ya Yadu

Idan baku manta ba, Gwamna Uba Sani ya ɗauki matasa 7,000 aikin 'yan banga domin su taimaka wa hukumomin tsaro a dawo da zaman zaman lafiya a Kaduna.

"Ku Daina Tura Matasa Zuwa Jihohin, Sokoto, Kebbi da Zamfara" Shinkafi Ga NYSC

A wani rahoton na daban kuma Tsohon shugaban kwamitin hukunta masu aikata laifukan 'yan bindiga a Zamfara ya shawarci hukumar NYSC.

Sani Shinkafi ya yi kira ga NYSC ta daina tura matasa 'yan bautar ƙasa zuwa wasu jihohi da 'yan bindiga suka hana zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262