Abin da Ya Sa Matatun NNPC Ba Za Su Taba Tace Danyen Mai ba Inji Obasanjo

Abin da Ya Sa Matatun NNPC Ba Za Su Taba Tace Danyen Mai ba Inji Obasanjo

  • Olusegun Obasanjo ya na ganin maganar matatar man Fatawal ta fara aiki a bana kanzon kurege ne
  • Tsohon shugaban kasar ya ce kamfanin Shell sun taba yi masa fada masa gaskiya game da matatun
  • Cif Obasanjo yake cewa rashin gaskiya da karancin girman matatun ne za su hana su dawowa aiki

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Olusegun Obasanjo ya san ciki da wajen Najeriya, a wata hira da aka yi da shi, ya zanta kan batun tattali da kuma matatun mai.

Cif Olusegun Obasanjo ya shaidawa The Cable cewa Bola Ahmed Tinubu ya yi kuskure da yake tunanin matatun mai za su fara aiki.

Tsohon shugaban na Najeriya ya musanya maganar cewa za a fara tace danyen mai a matatar Fatakwal nan da watan Disamban bana.

Kara karanta wannan

Bayan Cire Tallafin Fetur. Tinubu Ya Waiwayi Ma’aikata, Ya Koka Kan Albashin da Ake Biya

Obasanjo
Tsohin shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Obasanjo: "Yadda mu ka yi da Shell"

"Wani ya fada mani Tinubu ya ce matatu za su fara aiki a Disamba. Na fadawa mutumin matatun ba za su yi aiki ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ina fadan wannan ne tare da la’akari da bayanan da na samu daga kamfanin Shell a lokacin ina shugaban kasar Najeriya.
A lokacin ina shugaban kasa, na gayyaci Shell zuwa wani taro. Na fada masu ina son mika masu matatunmu, su kula da su.
Karara su ka fada mani cewa ba za su yi ba. Na yi mamaki, Na maimaita bukatata amma kuma su ka kafe a kan bakarsu."

- Olusegun Obasanjo

Gaskiyar zance a kan matatun mai

Bayan taron sai na fadawa mai gidansu (Babban darekta) ya jira ni domin mu yi wata ’ya magana.
Sai na tambaye shi meyasa su ka dage ba za su karbi matatun man ba. Sai ya ce mani ‘Ka na son jin gaskiyar lamarin?’

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Fito: Obasanjo Ya Bayyana Abinda Ya Sa Ya Ɗauko Umaru 'Yar'adua Duk Ya San Ba Shi Da Lafiya

- Olusegun Obasanjo

Obasanjo ya ce dalilai hudu kamfanin ya bada, na farko shi ne babu ruwansu da harkar. Na biyu, ba su aikin hako mai sai idan ta kama.

Na uku kuma sun ce akwai rashin gaskiya wajen tafiyar da matatun sannan na hudu, ana komawa manyan matatu a duniya ba kanana ba.

An rahoto shi ya ce matatun ba za su taba aiki ba muddin su na karkashin gwamnati.

A dalilin haka gwamnatin Olusegun Obasanjo ta saida su, Leadership ta ce Ummaru ‘Yar’adua ya na hawa mulki, ya soke cinikin a farkon 2007.

Obasanjo ya soki gwamnatin Buhari

Ana da labarin Olusegun Obasanjo ya ce yadda shiga-ya fita a lokacinsa, sai ga shi Muhammadu Buhari ya sa bashin Najeriya ya dawo sabo.

Tsohon sojan ya ce a duniyar da ake ciki a yau, dole sai kasar nan ta biya bashin kudin da ta karbo aro domin gwamnati ta rika yin facaka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng