Kotun Daukaka Kara Ta Bukaci Ma’aikatanta Su Zauna a Gida Yayin da Za a Yanke Hukunci Kan Nasarar Tinubu

Kotun Daukaka Kara Ta Bukaci Ma’aikatanta Su Zauna a Gida Yayin da Za a Yanke Hukunci Kan Nasarar Tinubu

  • Kotun sauraron kararrakin zabe za ta yanke hukunci kan shari'ar da ke kalubalantar nasar Shugaban Kasa Bola Tinubu
  • Hukuncin kotun shine zai tabbatar da wanda ya lashe zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairun 2023
  • Gabannin yanke hukuncin na ranar Laraba, 6 ga watan Satumba, kotun daukaka kara ta umurci ma'aikatanta da su zauna a gida

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Jaridar Thecable ta rahoto cewa an bukaci ma'aikatan kotun daukaka kara da su zauna a gida a ranar Laraba, wanda ya yi daidai da karar da za a yanke hukunci kan karar da ke kalubalantar nasarar zaben Shugaban kasa Bola Tinubu.

Kotun daukaka kara ta ba ma'aikatanta hutu ranar Laraba
Kotun Daukaka Kara Ta Bukaci Ma’aikatanta Su Zauna a Gida Yayin da Za a Yanke Hukunci Kan Nasarar Tinubu Hoto: @abati1990
Asali: Twitter

Da farko, Umar Bangari, babban magatakardar kotun, ne ya sanar da shawarar da kotun zaben shugaban kasar ta yanke na zartar da hukunci a ranar 6 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP Ya Rantsar da Sabbin Shugabannin Kananan Hukumomi 18 da Suka Lashe Zaɓe a Jiharsa

Bangari ya ce:

"A kokarin inganta gaskiya da yin komai a bayyane, za a watsa shirin yanke hukuncin kai tsaye ta gidajen Talabijin masu sha'awar haka don jama'a su bibiya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Sai an tantance mutum kafin ya samu shiga harabar kotun.
“Mutanen da aka tantance kamar su lauyoyi da wakilan jam’iyyun siyasa ne kawai za a ba damar shiga harabar kotun.
"An shawarci jama'a da su kalli yadda abun zai gudana a talabijin dinsu."

Ma'aikatan kotun daukaka kara za su zauna a gida a ranar Laraba

A wata takarda dauke da sa hannun Oluwaleye David, a madadin babban magatakardar, an umarci ma’aikatan kotun da su zauna a gida domin yin abubuwa cikin lumana a yayin zaman kotun, rahoton BusinessDay.

Sanarwar ta ce:

"An umurce ni da na sanar da dukkan ma'aikatan hedkwatar da Abuja da su zauna a gida a ranar Laraba, 6 ga Satumba, 2023.

Kara karanta wannan

A Karon Farko, Tinubu Ya Yi Martani Game Da Shari'ar Zabe Tun Bayan Saka Ranar Hukunci, Ya Ce Ko A Jikinsa

“Wannan ya kasance ne don samar da yanayi mai kyau da kwanciyar hankali a wannan zama na musamman da kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa a sashin kotun Abuja za ta yi.
“Saboda haka, an shirya matakan tsaro sosai don kula da kofar shiga kotun da ma dukkan muhimman wurare na harabar kotun.
“Bugu da kari, ma’aikatan da ke dauke da tambari wanda hukumar ta bayar ne kadai za a ba izinin shiga harabar kotun. Don Allah ku lura kamar yadda aka yi umurni."

Tinubu ya magantu kan shirin yanke hukunci a kotun zabe

A wani labarin, mun ji cewa yayin da ake dakon jiran hukuncin kotu na zaben shugaban kasa, Shugaba Bola Tinubu ya ce shi kam ko a jikinsa bai damu ba.

Hadimin shugaban a bangaren yada labarai da hulda da jama’a, Ajuri Ngelale shi ya bayyana haka a yau Litinin 4 ga watan Satumba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng